Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Katsina ta ware Naira miliyan 366 wajen samar da tashar FM rediyo a jihar.
Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu Dr Salisu Bala zango ya sanar da haka a lokacin da yake kare kasafin kuɗin ma’aikatar sa na 2026 a gaban ma’aikatan kasafin kuɗi da tsare-tsare na jihar.
Ya bayyana cewa har an sami amincewar kafa gidan rediyon ga aka sa ran kafin ƙarshen shekaran nan an kammala aikin ginin.
“Muna shirye shiryen tabbatar da ganin gidan rediyon ya fara aiki kafin kashen wannan shekara,”Inji Dr Bala Zango.
Kwamishinan ya ce ana sa ran da zarar gidan rediyon ya fara yaɗa shirye shirye, za a cimma kudin shiga da aka tsara za a samu.
Ya yabawa gwamna Dikko Raɗɗa bisa umurnin da ya bai wa ma’aikatu da hukumomi na gwamnatin jihar da su rinƙa mu’amala da gidan rediyon ta hanyar bada tallace tallace.
Zango ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa duk kuɗaɗen shiga da gidan rediyon zai sami kobo ɗaya ba zai ciwon kai ba,”za a tabbatar da gaskiya da adalci.
Kwamishinan ya sanar da cewa gwamnatin jihar za ta sanya wutan lantarki mai amfani da hasken rana a tashar gidan rediyon AM na jihar da ƙaramin tashar da ke garin Dutsinma domin magance matsalar rashin wutan lantarki na KEDCO.
