Ɓatar tiriliyan N210: Majalisar Dattawa ta matsa bincike yayin da NNPC ya buƙaci ƙarin lokaci

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Dattawa ta bayyana cewa Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) ya buƙaci a ba shi ƙarin lokaci na ya fitar da cikakken bayani game da zargin ɓatar Naira tiriliyan 210 daga cikin kuɗin kamfanin tun daga shekarar 2017 zuwa 2023.

Kwamitin majalisar akan asusun ƙasa (SPAC) ya bayyana haka, wanda a halin yanzu ya ke gudanar da bincike akan batun bayan da ofishin Antoni Janar ya nemi a bankaɗo rahoton kuɗin NNPC bisa zargin sauya akalar wasu maƙudan kuɗaɗe.

A watan Yuli ne kwamitin ya gayyaci Shugaban NNPC, Bayo Ojulari inda ya ba kamfanin mako uku na ya fitar da gamsassun bayanai akan wasu tuhume-tuhume 19 da aka gabatar masa da ke da alaƙa da ɓatar kuɗaɗen.

Baya ga haka, NNPC ya nemi a ƙara masa lokaci na ya haɗa rahoto akan lamarin, inda kwamitin ya amince da hakan, amma duk da haka har yanzu ba su cikakken bayani a kai ba.

Da yake ganawa da manema labarai a ranar Talata, shugaban kwamitin kuma Sanatan Nasarawa ta Yamma, Aliyu Wadada ya ce zuwa yanzu kamfanin ya miƙa rahotonsa game da tambayoyi 19 da aka gabatar masa saidai bai kai ga yin nazari a kai ba.

Ya kuma tabbatar wa al’umma cewa za,a yi adalci akan al’amarin wajen gabatar da rahoto mai zurfi bisa gaskiya da zarar an kammala nazari a kai.

By Babaji