Atiku, Sowore da wasu na shirin yin gangamin sako Nnamdi Kanu a Fadar Shugaban Ƙasa

Spread the love

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya haɗa kai da ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan-adam kuma tsohon dan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, wajen kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta sakin shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Atiku ya bayyana a shafinsa na X cewa ci gaba da tsare Kanu “tabo ne ga amincin Nijeriya da bin doka da oda.”

Kanu yana fuskantar tuhuma kan ta’addanci, cin amanar ƙasa, da tayar da fitina a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja — kuma tun shekaru da dama yana tsare duk da cewa kotuna da dama sun bayar da umarnin a sake shi.

Atiku, wanda shi ma tsohon dan takarar shugaban kasa ne a jam’iyyar PDP, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga yakin neman sako Kanu da Sowore ke jagoranta.

A kwanakin baya, Atiku ya nuna sha’awarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a ADC a 2027, inda ya bayyana cewa ba zai ja da baya ga kowa ba, tare da hada kan wasu manyan ‘yan adawa domin kalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

“Mun gaza a matsayinmu na ‘yan ƙasa idan muka bar wannan batu ya zama ciwon da ƙasa ta kasa warkewa daga gare shi.’”

A nasa ɓangaren Sowore a ranar Laraba ya buƙaci gwamnonin kudu maso gabas, ‘yan majalisa, sarakuna da malamai su shiga zanga-zangar da ake shirin yi don neman a sako Kanu.

Ya kuma ce, ya tuntuɓi fitattun ‘yan siyasa daga yankin, ciki har da Peter Obi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a 2023, domin su mara wa tafiyar baya yayin da suke shirin gangami nuna rashin amincewarsu ga cigaba da tsare Kanu.

By Babaji