Soja ya rasu bayan matarsa ta banka masa wuta

Spread the love

Wani jami’in soja ya rasa ransa bayan ya samu munanan raunuka sakamakon zargin matarsa da cinna masa wuta a yayin da suke cikin faɗa a gidansu da ke jihar Akwa-Ibom.

Rahotanni sun bayyana cewa, yayin da rikici ya ɓarke a tsakaninsu ne sai matarsa ta watsa masa fetur a jikinsa, sannan ta cinna masa wuta.

Sojan ya sha fama da raunuka masu tsanani na ƙona kana daga bisani ya rasu.

Akan haka ne aka garzaya da shi asibiti domin ba shi kulawa saidai duk da ƙoƙarin likitoci, ƙonewar ta yi tsananin da ya sa suka gagara ceto shi.

Jami’an tsaro sun tabbatar da faruwar lamarin, kuma tuni aka kama matar da ake zargi domin bincike a kai.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya samo asali ne daga rigimar cikin gida tsakanin ma’auratan sakamakon zargin cin amanar aure.

Wata majiya ta ce, lamarin ya faru ne a Wellington Bassey Barracks da ke Ibagwa, karamar hukumar Abak, a jihar Akwa Ibom, inda ma’auratan ke zama bayan auren su da aka yi cikin biki mai kayatarwa a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato a watan Afrilu, 2025.

An ruwaito cewa, matar ta gano wasu saƙonnin waya a wayar mijinta, waɗanda ta yi zaton daga wata mace ne, sai aka samu tashin hankali tsakaninsu. Duk da cewa Lt. Haruna ya musanta cewa yana wata alaka ta soyayya da wata, matarsa mai kishi ta yi masa mummunan abin ne yayin da yake barci — ta zuba masa mai ta kuma kunna wuta.

Wata majiya daga cikin barikin sojoji, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta bayyana cewa Lt. Haruna, wanda kuma likita ne kuma tsohon ɗalibin Jami’ar Jos, yana aiki ne a lokacin a matsayin Regimental Medical Officer (RMO) a Battalion na 6.

“Jami’in ya samu mummunan konewa, an garzaya da shi asibitin soja da ke barikin don kulawa da gaggawa, kafin daga bisani a tura shi zuwa University of Uyo Teaching Hospital domin ƙarin jinya”,inji ta.

By Babaji