AIT Farms ta tallafa wa ɗaliban Gombe da ƙwai 3,000 a bikin Ranar Ƙwai ta Duniya

Spread the love

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe

A yayin bikin ranar ƙwai ta duniya, kamfanin AIT Integrated Farms da ke Gombe ya gudanar da wani shiri na musamman inda ya raba ƙwai guda 3,000 ga ɗaliban makarantun firamare domin tallafawa lafiyar yara da inganta abincinsu mai gina jiki.

Shugaban kamfanin, Abubakar Inuwa Tata, ya bayyana cewa wannan aikin alheri yana nuni da yadda AIT Farms ke ɗaukar nauyin inganta abinci da bunƙasa tattalin arzikin al’umma ta hanyar tallafawa yara da manoma.

Ya ce, “Mun ɗauki nauyin koyar da manoma 100 na gida sabbin dabarun kiwon kaji tare da basu kaji domin su ƙara samar da abinci mai kyau da kuma samun riba.”

A nata ɓangaren, jakadiyar kamfanin, Hon. Hauwa Saraki, ta ce rabon ƙwai ɗin na nufin ƙarfafa halin cin abinci mai gina jiki a tsakanin yara, musamman waɗanda iyayensu ba su da isasshen hali.

“Wannan shi ne karo na biyar da AIT Farms ke bikin ranar ƙwai a Gombe tare da ɗaliban makarantu. Manufarmu ita ce mu tabbatar cewa kowane yaro ya ci aƙalla kwaya ɗaya na ƙwai a wannan rana ta musamman,” in ji ta.

Ta kuma yi kira ga masu hannu da shuni da ƙungiyoyin taimako su kwaikwayi AIT Farms wajen tallafawa shirye-shiryen da ke bunƙasa lafiyar yara da ilimin su.

Wasu daga cikin ɗaliban da suka amfana sun bayyana farin cikinsu tare da gode wa kamfanin bisa wannan kyakkyawan aiki.

Ana gudanar da ranar ƙwai ta duniya a duk shekara a ranar 10 ga Oktoba, domin wayar da kan jama’a game da muhimmancin ƙwai a matsayin abinci mai araha, mai gina jiki, da kuma sauƙin samu.

By ukarofi