Yadda Tinubu ya ji da zargin takardar bogi na tsohon Ministan Kimiyya ta bayan fage

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sababbin bayanai sun bayyana akan yadda Shugaba Bola Tinubu ya umarci tsohon Ministan Ƙirƙira, Kimiyya da Fasaha, wato Cif Uche Geoffrey Nnaji da ya yi murabus sakamakon zargin sa da yin amfani da takardar digiri ta bogi, lamarin da ya haddasa faɗi-in-faɗa acikin al’ummar Nijeriya.

A cewar sakamakon bincike, an gano cewa saukar ministan daga muƙamin umarni ne kai-tsaye daga shugaban ƙasa ba domin raɗin kai ba kamar yadda wasu kafafen labarai suka ruwaito a baya.

Hakan na zuwa ne bayan samun waɗansu rahotanni da ke zargin Cif Nnaji da miƙa takardun kammala karatu da hidimar ƙasa na bogi a yayin tantance shi a matsayin minista a shekarar 2023.

A ƴan kwanakin nan aka zargi tsohon ministan da yin amfani da digirin bogi daga Jami’ar Nijeriya ta Nsukka, lamarin da ya ja hankalin al’umma, duk da cewa ya musanta lamarin.

Nnaji ya bayyana cewa, ana masa bita da ƙulli ne, inda ya zargi abokan hamayyarsa a siyasa da yunƙurin ɓata masa suna.

A ranar Talatar da ta gabata ne Nnaji ya fitar da saƙon murabus ɗin nasa daga muƙamin ministan bayan cecekuce ya ɓarke game da rashin tabbas na takardarsa ta digiri daga Jami’ar Nijeriya ta Nsukka (UNN) da kuma ta kammala NYSC.

Duk da cewa ya yi ikirarin kammala digirin farko a UNN a shekarar 1985, rahotanni sun bayyana cewa jami’ar ta gaza tantance shi a matsayin ɗaya daga cikin ƴaƴan da ta yaye, lamarin da ya janyo cecekuce da kushe acikin al’umma.

Saidai duk da wannan ikirari, majiyoyi daga Fadar Shugaban Ƙasa sun shaida wa manema labarai cewa tun a farkon satin ne Tinubu ya gayyaci ministan zuwa fadar cikin sirri inda ya ni ya yi murabus domin kare martabar gwamnatinsa.

Wani babban jami’in gwamnati ya bayyana cigaba da zama a ofis ga tsohon ministan a matsayin tozarci ga kima da darajar Gwamnatin Tarayya.

By Babaji