
Wani ƙaramin jami’in ƴan sanda mai suna Ukasha Muhammed mai lambar aiki F/No 533164, ya rasa ransa sakamakon cacar baki tsakaninsa da sojoji a shingen bincike.
Al’amarin ya auku ne a yankin Bayan Gari da ke cikin gar Bauchi a jihar Bauchi, ranar Juma’a.
Bisa ga bayanan da aka tattara, wani soja da ke aiki a ƙarƙashin Hadaddiyar Rundunar Sojoji da ƴan Sanda (Operation Safe Haven) ~ wacce ke kula da zaman lafiya a Jihar Filato da wasu sassan Bauchi da Kaduna, ya samu saɓani da jami’an ƴan sanda a wani shingen duba ababen hawa (check point).
Wata daga cikin dangin mamacin mai suna Rashida Muhammed ta shaida wa majiyar mu “cewa lamarin ya faru ne a ranar Jumma’a, 10 ga Oktoba, 2025, a unguwar Tudun Wadan Dan Iya da ake kira Bayan Gari, a cikin birnin Bauchi.”
Ta ce, a wurin akwai motar sintirin ƴan sanda da ke tsaye domin sa ido a wajen da ake gudanar da taron jama’a.
Rashida ta bayyana cewa matsalar ta fara ne da misalin ƙarfe 9 na dare, lokacin da jami’an sintiri suka tsaya suna binciken motocin da kuma masu babura. A cewarta, a wani lokaci wani mutum ya ƙi bin umarni, ya hana su aiki yadda ya kamata, lamarin da ya jawo ɗan ɗaga murya da hayaniya.
Bayan kusan awa ɗaya, sojan ya dawo wurin tare da wasu abokansa biyu. Kafin a ce komai, sai aka harbi Ukasha a kirjinsa.
Ta ƙara da cewa lokacin da mutane suka fara gudu daga wurin, wasu suka taru suka cafke ɗaya daga cikin sojojin, kafin runduna ƴan sanda ta ƙara ƙarfin jami’ai ta isa wurin ta kama su.
Rundunar ƴan Sanda ta Jihar Bauchi ta tabbatar da aukuwar lamarin.
Kwamishinan ƴan sanda, Sani-Omolori Aliyu, ya buƙaci jami’ansa su kwantar da hankali tare da jaddada muhimmancin gudanar da cikakken bincike don gano gaskiyar abin da ya faru da mutuwar Ukasha.
A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar (PPRO), CSP Mohammed Ahmed Wakil, ya fitar, ya bayyana cewa:
“A ranar 10 ga Oktoba, 2025, da misalin ƙarfe 10:35 na dare, rundunar ta samu rahoton cewa yayin sintiri na yau da kullum a yankin Bayan Gari, jami’an sintiri ƙarƙashin jagorancin Inspector Hussaini Samaila sun gamu da hari kan ɗaya daga cikin jami’ansu, Constable Ukasha Muhammed, a gaban Padimo Hotel, daga wasu mutane biyu.”
Wakil ya ce an gano ɗaya daga cikin mutanen da aka kama a wurin da sunan Private Usman Mubarak (23NA/84/5346), soja ne daga rundunar STF Operation Safe Haven, Jos ~ Jihar Filato.
Bayan kusan ƙarfe 11:05 na dare, wasu sojoji biyu ~ Private Yakubu Yahuza (23NA/85/10185) da Private Godspower Gabriel (23NA/84/5654) ~ waɗanda ke sanye da riga amma ba cikakken kakin soja ba, kuma ɗauke da bindigogi, sun iso wurin suka harbi Ukasha a kirji na hagu, suka tsere daga wurin.
Bayan haka an garzaya da Ukasha zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) a Bauchi, inda aka tabbatar da rasuwarsa.
An kai gawarsa dakin ajiye gawa, sannan rundunar ƴan sanda ta kama Yakubu Yahuza da Godspower Gabriel.
An kafa ƙungiyar binciken kisa ta musamman wadda ta ƙunshi gogaggun masu bincike, domin gudanar da bincike mai zurfi da tsanaki, tare da tattara shaidu da tabbatar da adalci cikin tsari da ƙwarewa.
