Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya bayyana cewa tattalin arzikin Nijeriya na samun ci gaba a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai cewa hakan alama ce ta ci gaba a tafiyar ƙasar.
Akume ya faɗi haka ne a yayin ƙaddamar da taron ƙungiyar Shugabannin Kiristoci ta Arewacin Nijeriya (NOCRELA) da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa taken taron shi ne “Rawar da shugabannin Kirista ke takawa wajen gina ƙasa.”
Akume ya ce, tattalin arzikin ƙasar ya nuna alamun inganta, inda ya ambaci cewa tattalin arzikin cikin gida ya tashi da kashi 4.4%, yayin da ajiyar kuɗin ƙasashen waje ya kai dala biliyan 42.
Ya buƙaci ’yan Nijeriya su haɗa kai wajen gina ƙasa, yana mai yaba wa Shugaba Tinubu bisa yadda yake aiki tare da mutane masu bambancin addini da asali.
“Shugaban ƙasa Musulmi ne, amma yana mu’amala da kowa — Kirista, Musulmi da masu bin addinan gargajiya — ba tare da wariya ba,” inji shi.
“Nijeriya ƙasa ce mai girma, tana tafiya da sauri zuwa tudun mafarki. A karkashin jagorancin Tinubu, muna kan hanya madaidaiciya kuma alamu sun fara bayyana.”
Akume ya kuma sake jaddada saƙonsa na bikin cika shekaru 65 da samun ’yancin kai, inda ya ce Nujeriya “na tafiya gaba” kuma “ana cika alƙawari.”
Ya yaba wa masu shirya taron NOCRELA bisa hangen nesa da jajircewarsu, yana mai cewa cocin na da muhimmiyar rawa wajen wanzar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa.
“Gwamnati tana fahimtar cewa jagorancin ruhaniya yana da matuƙar muhimmanci wajen gina al’umma mai kima da ɗabi’a,” inji Akume.
Ya bayyana tabbaci kan ƙoƙarin gwamnati na magance matsaloli da tallafa wa matasa, tare da kira ga coci da ta ci gaba da taka rawa wajen inganta dabi’u da tunanin ƙasa.
A nasa jawabin, shugaban ƙasa na NOCRELA, Archbishop JohnPraise Daniel, ya ce ƙungiyar na wakiltar muryar Kiristocin arewacin Nijeriya gaba ɗaya, domin su haɗa kai da yin magana da murya ɗaya wajen kawo ci gaba.
Ya jaddada muhimmancin haɗin kai da fahimtar juna a tsakanin shugabannin Kirista a arewa, yana mai cewa suna da niyyar ƙarfafa zaman lafiya, adalci da ci gaba.
Archbishop Daniel ya kuma yaba wa gwamnatin Tinubu bisa ƙoƙarinta na kawo haɗin kai wajen naɗin manyan muƙamai, inda ya ce akwai Kiristoci da dama a muhimman wuraren gwamnati a yanzu.
