Yajin aikin ASUU: Shugaban NELFUND ya bayyana abinda zai faru da lamunin ɗalibai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Asusun Bada Lamuni ga Ɗalibai (NELFUND) Akintunde Sawyerr, ya ce yajin aikin ƙungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ba zai shafe ayyukansu ba.

Sawyerr ya bayyana haka ne a yayin hira da gidan talabijin na Channels a safiyar yau Talata.

A cewarsa, tattaunawar da ake yi tsakanin wakilan Gwamnatin Tarayya da na ASUU ƙarƙashin jagorancin Ministan Ilimi Dakta Tunji Alausa zai haifar da ɗa mai ido.

Shugaban na NELFUND ya ƙara da cewa, ofishinsa yana fatan shirin ma’aikatar zai samar da sakamakon mai kyau duba da tsarin da aka ɗauka na ƙoƙarin tabbatar da gaskiya da adalci acikinsa.

Ya kuma ce, ofishin nasa ba zai so wani tsaiko sakamakon yajin aiki ya shafi ɗaliban ba, yana mai alƙawarin sanar da dukkan wani abinda ya taso a yayin da suke sanya ido a kai.

By Babaji