
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta fara yunƙurin aiwatar da dokar ‘ba aiki ba albashi’ a jami’o’i biyo bayan umarnin da ta bayar na a ƙirga dukkanin malaman jami’o’in da ke jami’o’in tarayya.
A wata takarda da Ministan Ilimin ya fitar da ke ɗauke da kwanan wata 13 ga watan Oktoba, 2025 da aike wa jagororin jami’o’i da manyan masu ruwa da tsaki a fannin ilimi, gwamnatin ta jaddada matsayarta akan dokar ba aiki ba albashi.
Haka kuma, an aika takardar ga Shugabar Ma’aikatar Ma’aikata da Akanta-janar na Ƙasa da kuma Sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i (NUC).
A cewar takardar, an umarci kowane shugaban jami’a ya gudanar da tantance malaman da ke aiki ta hanyar ƙirga waɗanda suke zuwa aiki da kuma wanda bai zo ba.
Haka kuma ministan ya bayyana rashin jin daɗin gwamnati kan matakin da ASUU ta ɗauka na tsunduma a yajin aikin duk da ƙoƙarin fa gwamnatin tarayyar take yi biya buƙatun da aka cimma yarjejeniya akansu da ƙungiyar.
