Daga BAMAI A. DABUWA KKM
Sunan Littafi: Asalin Labarina.
Marubuci: Ayuba Muhd Danzaki.
Shekarar Bugu: 2022.
Bugu: AGP Computers Fagge.
ISBN: Babu.
Shafi: 144.
Yanayi: Damina.
Jigo: Soyayya da Zamantakewa.
Salo: Fagen Waje.
Mai Sharhi: Bamai A. Dabuwa Kkm.
Gabatarwa/Tsokaci:
‘Asalin Labarina’, labari ne na wani matashin mai kuɗi Ziya’u wanda ya haɗu da matsalolin rayuwa kala-kala. Matsalolin da idan aka jarrabi jahili da su sai ya ɗaga kai sama da cewa wai me na maka ne? Duk da haka shi ya yi haƙuri, kodayake, ya mutum zai yi da abin da ya fi ƙarfin wuta wai inji kishiyar ƙonanniya. Daga ƙarshe Allah ya kuɓutar da shi tare da kyautata rayuwarsa. Lafiyayyen labari ne da iyaye za su iya siya da barin yaransu su karanta. Dangane da marubucin kuwa, ba ya buƙatar gabatarwa, abu guda kawai za mu ce shi ne ya amsa sunansa Zakin Marubuta.
Kura-kurai:
Masu iya magana suka ce duk wanda ya ce bai taɓa yin kuskure ba, to bai tarki yin wani abu sabo ba ko kuma ma bai taɓa yin komai ba. Ke nan, ba kuskure ba ne don ka kuskurewa wani al’amari. Sai dai, hakan ba zai taɓa sa wa kuskuren ya zama daidai ba. Salon da aka yi amfani da shi rago ne, sannan ya rasa kusan kowace kamala ta rubutu. Idan ka ɗauke ƙa’idojin rubutu, to babu wata ƙa’ida ko tsari na haɗaɗɗen labari da ba a karya sau biyar zuwa goma ba. Misalin karɓuwa da haɗewar wannan littafi kamar misalin wani shiri ne da ka taɓa kalla a lokacin yarinta, amma da za ka maimaita kallonsa yanzu sai ka ɗauka lallai da ba ka da hankali. Ma’ana: wannan littafi na yara ‘yan primary zuwa secondary ne kawai domin yana matuƙar kama da yadda ake labarta tatsuniya. Har’ilayau, yana daga cikin gazawa ko raunin da wannan littafin ya samu yadda marubucin ke maimaita saƙo, labari ko magana ta yadda ma mai karatu na iya cafar me aka yi farko daga ƙarshen labarin ma. Ya cika dawurwuri dayawa. Sau uku ne kawai aka yi amfani da karin magana a duk labarin (51, 127 da 144). A sauƙaƙe idan har dalla-dalla za a yi da burtso da kowane kuskure a fili, sai sharhin ya zarta girman littafin sau kamar uku. Ga misalai kaɗan daga abin da muka tsinkaya.
1. Kuskuren ƙa’idojin Rubutu.
An yi matuƙar ƙoƙarin kiyaye abubuwa dayawa da suka shafi ƙa’idojin rubutu a littafin, musamman ɓangaren da ya shafi haɗewa da rabewar wasu kalmomin yadda ya kamata. Sai dai, a wasu wuraren an muzanta wasu dokokin sosai a wurare mabanbanta. Misali:
A. Dama maimakon da ma (6).
B. Fauwalawa maimakon fawwalawa.
Ire-iren wannan sun zo dayawa a littafin, duba shafi 16 da saura.
1.1. Kamar yadda yake a tsari cewa ana fara kowace jimla da babban baƙi ne, sannan a gaban duk wata aya, alamar tambaya da motsin rai ma ana farawa da babban baƙi, ba a kiyaye hakan ba a littafin wuri dayawa. Misali:
“Ke! na nuna ta hannu,…” (6)
“,…me ya sa ba kya jin magana ne? tun yaushe…” (6).
1.2. Wasu kalmomin da ake sa wa a cikin baka a wasu wuraren kuskure ne (babu buƙatar bakan). Misali:
A. (Honey) (7).
B. (Ayubkhan Restaurant Abuja ) (9).
Domin kuwa har sai idan an so fayyacewa ne za a sa su cikin bakan.
1.3. Ragi da ƙarin wasu baƙaƙen a wurare da dama, saɓanin kamatar su. Misali:
A. “,… saboda kyautarsa da kuma kyautatawar talakawa na ƙasa da shi.” (10)
Babu buƙatar baƙin r a gaban kalmar kyautatawa.
B. “,…tu da ya auro juya,…” (10)
Akwai buƙatar ƙarin baƙin n a jikin tu.
Ire-iren wannan sun zo a wurare masu yawa a labarin.
2. Tsawalla Bayani/Fayyacewa:
Yana daga abin da ke haifar da gundura a rubutu idan aka tsawaita ko raina fahimtar mai karatu. Har’ilayau kuskure ne a labarin da aka samar da shi da yaren Hausa kuma a shigo da wani yaren da nufin sauƙaƙawa mai karatu fahimta musamman bayan an riga an fayyace shi da ainashin yaren da aka samar da rubutun (Hausa).
Misali: Ya zo kamar haka a farkon labarin:
“Da yake lokacin damina (raining season) ne…” (4).
Babu buƙatar kawo kalmar raining season kuma cikin baka, domin daminar ta wadatar.
Har’ilayau, kuskure ne a wajen da aka aro kalma daga wani yare idan ba a Hausantar da ita ba a rubuce. Misali kalmar grass carpet (5), maimakon giras kafet. (Lura: idan ya kasance aro ne ke nan, amma idan fayyacewa ne to ba laifi ba ne).
3. Kufcewar Salo: Kufcewar salo na nufin kwafsawa, sakin layi, mantuwa, balla-balla ko shigar da bara a bana cikin rubutu. Matsalar kufcewar salo na lalata labari da haifar masa da rashin kan gado domin yana jirkiɗa ma’ana da isar da saƙon da ba shi ake nufi ko son isarwa ba. Kasancewar salo ya karkasu gida dayawa, kamar salon bayar da labari, azanci da saura. Kufcewar sa ma haka ne. Misali:
3.1. Kufcewar Salon Bayar Da Labari: Salon bayar da labari a rubutu guda biyu ne, akwai salo a cikin fage da kuma ba wajen fage. Na cikin fage shi ne wanda marubucin ya shiga cikinsa, wajen fage kuwa shi ne idan yana bayar da labarin wasu ne daban. An samu kuskure na kufcewar salo a wannan labarin da aka zaɓi gabatar da shi da salon waje sai kawai marubucin ya tsunduma ciki babu gaira babu dalili. Misali:
“Suka bi wata kyakkyawar hanya mai ɗauke da (grass carpet) a shimfiɗe a ƙasa,…”(5).
Sai kuma ya zo a gaba kamar haka:
“A hankali na ƙara karanta sunan wajen sayar da motocin…”(5).
Lura: Hakan ya kasance ne ba a cikin ƙauli ba.
3.1.1. Daga baya, marubucin ya shigo da salon ciki na bayar da labari, sai dai an samu matsala wajen ba shi dama fiye da ƙa’ida. A tsarin bayar da labari a cikin fage dole akwai abubuwan da mai bayar da labarin ba zai sani ba game da wasu taurarin, misali zancen zuci ko tunaninsu. Haka ba kowace magana tasu ba ce zai iya kawowa daidai, domin kuwa lokacin da abin ya faru ma ba haife shi ba.
3.2. Kuskurewa Azanci Da Salon Magana Da Azanci:
A shafi na 10, an bayyana Alhaji Rabi’u mahaifin Ziya’u a mai kuɗin gaske. Mutumin da tsabar wadata sama da likito biyar ne suke kula da matarsa lokacin da naƙuda ya kama ta (11). Sai kuma muka tsinkaya gaba kamar haka:
“Kafin takwas da kwata tuni Larai ta gama dafa shayi, ta zuba cikin (flask), sannan ta ɗauko leda mai sanda-sanda ta harhaɗa kayan shayi ta zuba kamar su; soyayyen dankali da wainar ƙwai.” (11).
Haba! Kamar Alhaji a sa wa matarsa abinci a leda kuma shi ne zai kai mata? To ko ni da ba ni da aure na san matar ƙanina ba za ta aiko min abinci a leda ba.
3.2.1. Har’ilayau ya zo kamar haka:
“Tana zuwa ya buɗe ƙofar kenan sai suka haɗa ido da Metron Suwaiba.” (13³).
Yana ne a wajen ba Tana ba domin ana nufin Alhajin idan aka yi la’akari da abin da ya gabata.
3.2.2. “Haka ake kowa ai ana so kafin ta mutu ya ga jikokinsa.” (14³).
Wannan maganar Mahaifiyar Alhaji Rabi’u ce, bayan kuma matarsa ta haihu.
3.2.3. A yadda marubucin ya bayyana arzikin Alhaji da kuma ƙawa da girman gidansa wanda yake ɗauke da su siwimin ful za ka ɗauka cewa ƙaramin inji bai kai ya wadaci gidan da wuta ba, sai irinsu MIKANO. Amma abin mamaki sai ga shi da mai ya ƙare wai an siyo galan (4 lita) an zuba. (18).
3.2.4. “Jibrin, Salamatu ta dawo gida ka san ta gama primary shi ne…” (23).
“Mun ɗauki dogon lokaci muna hirar soyayya, daga ƙarshe muka yi sallama ta shiga gida…” (25)
Wai yarinyar da ta gama primary ce har ta isa a zo wajenta firar soyayya. Wane mahaifin ne zai bar ‘yarsa.
3.2.5. A shafi na 11, an bayyana Larai a matsayin mai aiki a gidan Alhaji Rabi’u. Wace ke dafe-dafen abinci. Amma a gaba (59) sai marubucin ya manta da bayyana da Hajiya A’isha (matarsa) ita ce ke yin girke-girken. Wannan tufka da warwara ce.
4. Cushe.
A wasu wuraren marubucin ya yi amfani da dama wajen shigo da taurarin da mai karatu yana isa wajen zai fahimta wasu abokan mu’amalar marubucin ne na zahiri da aka ƙaƙaba a cikin labarin. Ba hakan ne kuskure ba face yadda aka shigo da su ɗin da wajen sam ba su dace ba. Misali:
“Tun daga wannan lokacin metron Suwaiba ta shiga ta miƙa mata…” (11).
Damuwar shi ne babu wanda ya san abin da aka buƙata har ta miƙa.
Kana yana daga kuskure faɗin marubucin kamar haka:
“,domin duk matar da take zuwa wannan asibitin (Malam Aminu Kano Teaching Hospital) to ƙarya take ta ce ba ta san Metro Suwaiba ba.”
Kalmar ƙarya a jimlar kuskure ne, domin ba lallai duk masu zuwa asibitin awo ne suka san ta ba. Kuma babban asibiti kamar wannan ba kullum take da duti ba. Wasu kuma ba ruwansu da sunanka, idan sau miliyan za ku haɗu ba lallai su iya sani ba.
5. Maimaita Kalma Ko Ma’ana (Tautology.
A wurare masu yawa marubucin ya yi amfani da kalma guda fiye da sau ɗaya a jimla wand ya haifar da rauni ƙarancin armashi wa jimlar. Shi ne dalilin da ya sa muka ce ta ko’ina ka datsi littafin za ka gane.
“…nake shiga idan na zo wanka na tsunduma na kama yin wanka kamar yadda na saba.” (19).
An maimaita ire-iren haka sau barkatai.
6. Kuskuren Aro Da Rubuta Kalma Daidai A Duk Yaren.
An fi so idan aka aro kalma daga wani yaren a Hausantar da ita a rubuce, idan kuma hakan bai samu ba to zai fi idan aka rubuta ta yadda take a waccan yaren da aka aro. Sai dai a wannan littafin an samu kuskure wajen kiyaye hakan, babu mamaki ƙarancin bincike ya haifar da hakan. Misali:
“…wacce take fama da ciwon tarin T.V.” (86).
T.B ne daidai ba T.V.
7. Idan ka cire suna, babu ta inda hoton bangon littafin yake da alaƙa ta kowace fuska da labarin.
Tambayoyi:
1. Me metron Suwaiba ta shiga ta miƙa mata? (11).
2. Wane ne daidai:
Metron Suwaiba? (11).
Metro Suwaiba? (11).
3. Yaushe soyayyen dankali da wainar ƙwai suka zama kayan shayi? (11).
4. Shin mahaifiyar Alhaji Rabi’u wane yare ce, domin yadda take Hausa kamar wace ta zo daga Borno duba da yadda take mayar da namiji mace ko mace namiji.
“Haka ake kowa ai ana so kafin ta mutu ya ga jikokinsa.” (14³).
5. “Ba farkon ta ɗauko ta zuba min ruwan juice,”. (17)
Me ake nufi da wannan jimlar.
6. Wace cuta ce cutar tarin T.ɓ?
ƙarƙarewa:
Ba lallai ne kowane mai karatu ya gamsu da duk abubuwan da muka zayyana a sama kuskure ba. Kuma ba lallai abin da muke yi wa kallon kuskure ne ya kasance kuskuren ba a zahiri. Musamman idan muka yi la’akari da faɗin cewa komai daidai ne, ya danganta da daga kusurwar da mutum ya kalla. Ya ishi kowa hujja cewa an gina wannan labari a kan tausayi ko taɓa zuciyar mai karatu, amma ƙila saboda kasancewar tawa zuciyar a daskare take ba a taɓa ni ba. Ke nan, wa masu lafiyayyiyar zuciya daidai ne idan suka yi watsi da duk wani ƙalubalena. Sai dai, zan so a inda aka fahimta na kuskure a nusar da ni.
Daga ƙarshe muna jinjina ga Zakin Marubuta bisa namijin ƙoƙarinsa wajen samar da wannan labari. Ya tafi da ni ainun musamman wajen da ya dawo da Zaliha har ta zama matar Ziya’u. Kuma gaskiya an yi aiki mai kyau a bugun littafin. Ina roƙon afuwa idan na tsaurara harshe domin Allah. Allah ya ƙara basira da ilmi mai amfani.
Na gode.
07037852514
