Kano ta haura zuwa mataki na huɗu daga na 35 a jihohin da suka fi ƙwazo kan aiwatar da dokoki kan sauyin yanayi a Nijeriya

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Jihar Kano ta samu babban ci gaba a jerin jihohin da suka fi kula da dokokin sauyin yanayi da ake kira ‘Subnational Climate Governance’ , inda ta haura daga matsayi na 35 zuwa na 4 a cikin jihohin Najeriya.

Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dakta Dahir M. Hashim ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Kano, yana mai cewa wannan nasara ta samo asali ne daga gyare-gyaren gwamnati da ƙarfafa cibiyoyi da kuma shirye-shiryen al’umma da suka gina tsarin kula da sauyin yanayi mai dacewa da buƙatun duniya da na cikin gida.

A cewar Hashim, gwamnatin jihar ta faɗaɗa ababen more rayuwa masu dacewa da yanayi, ta kuma zurfafa tsarin kula da muhalli ta hanyar aiwatar da manufar sauyin yanayi ta Jihar Kano.

Ya ce shirin amfani da sabbin hanyoyin makamashi a hukumomin gwamnati da ƙawata birane da bishiyu ƙarƙashin shirin sabunta tituna da kuma dashe-dashen bishiyoyi da hana zaizayar ƙasa sun taka muhimmiyar rawa wajen kai jihar wannan matsayi mai girma.

“Waɗannan shirye-shirye sun shimfiɗa tubalin juriya da canji zuwa makamashi mai tsafta, da ci gaba mai ɗorewa,” in ji Hashim.

Kwamishinan ya ƙara da cewa wannan girmamawa shaida ce ta haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatar da gundumomi da shugabannin al’umma da ƙungiyoyin farar hula, da abokan hulɗa da suka haɗa kai wajen ƙarfafa matakan yaƙi da sauyin yanayi a Kano.

By ukarofi