Gudunmawar marubuta ga cigaban ƙasa

Spread the love

Daga JIBRIN YUSUF KAILA

A yayin da ýan Nijeriya ke cigaba da bayyana farincikinsu da murna albarkacin cika shekaru 65 da samun ýancin kan Nijeriya daga turawan mulkin mallaka na ƙasar Ingila, lallai ya kamata mu tambayi kawunanmu, wacce gudunmawa ce marubuta ya kamata su taka don samar da cigaban ƙasa? 

Tabbas muna cikin wani lokaci da Nijeriya ke cikin buki da murna, ya zama wajibi ga kowanne ɗan ƙasa nagari, ya yi nazari da kyau don tunawa da gwagwarmayar da mazan jiya suka yi wajen samar wa ƙasar nan ‘yancin kai. Dole mu kasance masu duba abin da ya gabata da abin da muke ciki. ‘Yanci shi ne ginshiƙin rayuwa, kuma duk wanda ya fahimci ma’anarsa ya san cewa ba kawai kyauta ba ne, hakkin mu ne bakiɗaya. 

Kamar yadda muka sani ‘yancin ɗan ƙasa yana tattare ne da tunawa da tarihi, koyo daga darussan baya, da kuma fatan kyautata gobe. Saboda haka, wajibi ne a godewa Allah da Ya bamu damar rayuwa cikin wannan lokaci, duk kuwa da ƙalubale da matsaloli da ƙasar mu ke fuskanta a yau.

Idan aka yi dubi cikin tsanaki, a cikin kowane rukuni na al’umma akwai masu taka muhimmiyar rawa wajen tasiri na tafiyar da ita. Daga cikin waɗannan rukuni, marubuta suna da matsayi na musamman. Marubuci ba wai mai rubuta kalmomi ba ne a karanta ko a yi nishaɗi kawai, shi madubi ne ga al’umma, don shi ne mai ɗaukar tarihin jiya da yau domin gobe. Mai haskaka gaskiya da nuna kura-kurai, da kuma sauya tunanin jama’a ta hanyar hikima.

Rubuce-rubucen da marubuci kan yi, idan aka sarrafa su ta yadda ya dace cikin basira da ilimi, suna kawo sauyi mai girma da muhimmanci ga al’umma. Kamar yadda muke gani daga kallon finafinai masu dogon zango da muke yi yau da gobe, saboda tasirinsu cikin zuciyar mai kallo, da suke motsa al’umma daga rashin fahimta zuwa fahimta, daga jahilci zuwa wayewa.

A cikin ƙasashen da suka ci gaba, marubuta suna taka muhimmiyar rawa wajen kawo sauyi ga al’ummarsu. Labaransu, kundin tarihin su, da har ma zantukan su sun kasance kayan tunatarwa da gyara ga shugabanni da talakawa. Idan muka dubi masana’antar finafinan Indiya ta Bollywood, za mu ga yadda suke cusa jigogi masu ma’ana a cikin labaran soyayya tare sarkewa cikin ilimi na kishin ƙasa da zamantakewar su, ba soyayya kaɗai suke bai wa muhimmanci ba, suna kuma isar da saƙonni na tarihi, kishin ƙasa, gwagwarmayar kawo sauyi a siyasa da rayuwa, da sauran batutuwa masu matuƙar muhimmanci ga al’ummar su. Wannan shi ya sa finafinansu suka zama wani abin kallo a duniya musamman a yankinmu na Afrika da duniya bakiɗaya. Duk da yake dai mu ma a namu finafinan akwai waɗanda suke ba da gudunmawa wajen faɗakarwa da wayar da kai, don samar da sauyi ga sha’anin zamantakewa da shugabanci, kamar irin su shirin nan mai dogon zango, mai suna ‘Kwana Casa’in’ wanda ake nunawa a Arewa24, da kuma irin su ‘Manyan Mata’ wanda Abdul Amart ya ɗauki nauyin shiryawa. 

Saboda haka, marubuta a cikin al’umma suna da nauyin da ya fi na nishaɗi ko kwaikwayo. Ya kamata su riƙa yin rubutun da za a nuna wa al’umma gyara da kuma mafita akan abin yake wakana a ƙasarsu, su tsinci ƙasa, tattalin arziƙi da zamantakewa ta hanyar kawo jigogi masu ma’ana. Rubuce-rubuce masu ƙarfafa kishin ƙasa, tunatar da tarihin gwagwarmayar da aka yi domin samun ‘yanci, da kuma fito da matsalolin yau da kullum cikin hikima da ƙwarewa, su ne rubuce-rubucen da za su ba da gudummawa wajen farfaɗo da ƙasa.

Idan al’umma ta mai da hankali wajen  rubutun labaran  gyara to, marubuci zai zama mai tsara makoma. Yana iya zama murya ga marasa murya, haske ga rayuwar da take cike da duhu. Wannan shi ne babban dalilin da ya sa marubuci bai  kamata ya taƙaita kansa ga rubuce-rubucen soyayya kawai ba, duk da cewa soyayya ita ma ɓangare ce ta rayuwa, amma ya kamata ya mayar da hankali wajen rubutun da zai jawo hankalin jama’a ga makomar ƙasar da ke gabansu.

Marubuci ya kamata ya kasance mai tunani akan makomar al’ummarsa, mai tuna musu da tarihin su, mai jawo hankalinsu zuwa gaskiya, kuma mai ƙarfafa wa shugabanni gwiwa, wajen ɗaukar matakan da za su inganta rayuwar jama’a. Duk al’ummar da ba ta bai wa marubutanta muhimmanci ba, tana asarar wani babban haske a rayuwarta. Don haka, wannan rana ta musamman tana da darasi mai girma. 

Ku girmama kalmar marubuta, ku karanta rubuce-rubucensu, ku kuma ɗauki darussan da suke isar mana domin ganin an samu cigaba mai ɗorewa.

Barka da Ranar Yancin ƙasa.

By ukarofi