
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya miƙa gaisuwar ta’aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar Kenya bisa rasuwar tsohon Fraministan ƙasar, Raila Odinga.
A takardar da Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar a yau Laraba, Tinubu ya bayyana Odinga a matsayin ginshiƙi a siyasar Afirka.
Ya kuma yaba da sadaukarwarsa ta tsawon lokaci ga harkar dimukraɗiyya, shari’a da haɗin kai, yana mai cewa ya bar tarin alkhairai a ƙasarsa Kenya da ma Afirka baki ɗaya.
Haka kuma, ya jinjina masa bisa ƙoƙarinsa wajen kawo sauyi a harkar zaɓe musamman wajen shugabancin da ya bai wa al’umma muryar faɗa-a ji.
Kazalika, Tinubu ya yabe shi akan gudumawar da ya bayar na haɗa kan ƙasashen Afirka da haɗin kai tsakanin shiyyoyin Nahiyar.
Har’ilayau, Tinubu ya yi fatan alkhairan tsohon fraministan su cigaba da tasiri wajen samar da zaman lafiya, haɗin kai da ci-gaba a ƙasar.
