Majalisar Dokokin Katsina ta amince da kasafin kuɗin cike giɓi karon farko na shekara ta 2025

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Majalisar ta amince da kasafin kuɗin cike giɓi a karon farko na shekara ta 2025 da ya kai Naira biliyan ɗari da talatin da bakwai da miliyan dari biyar da talatin da tara da dubu ɗari shidda da ashirin da huɗu da naira dari da saba’in da ɗaya da kwabo ashirin da huɗu.

Shugaban majalisar Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura ya bayyana haka jim kaɗan bayan amincewa da rahoton kasafin kuɗin da kuma yiwa ƙudurin dokar karatu na uku.

Shugaban kwamitin Hon Lawal Yaro ya ce ƙaramin kasafin kuɗin bai canza kasafin kuɗi na 2025.

Yace a cikin jimlar kasafin kuɗi na 2025 aka matso da karamin kasafin kuɗin.

Shugaban masu rinjaye Hon Shamsuddini Abubakar Dabai da ya ƙare karatu na uku na dokar yace ƙaramin kasafin kuɗin zai taimakawa gwamnatin Malam Dikko Raɗɗa ta ƙaro ɓullo da ayyukan alheri.

Gwamna Dikko Raɗɗa har ya rattaɓa hannu a kasafin kuɗin da ‘yan majalisar su ka amince.

By ukarofi