Matsin rayuwa ya kusa zama tarihi a Nijeriya, inji Shettima

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya tabbatar wa al’ummar Nijeriya cewa ƙuncin tattalin da suka samu kansu a ciki na gab da zama tarihi yayin da ƙasar ke shiga sabon shafi na nasarorin harkar tattali da bunƙasarsa a ƙasar.

Da yake jawabi a taron ƙungiyar harkar makamashi ta ‘Renewable Energy Innovation Forum’ (NREIF) a Abuja ranar Talata, Shettima ya ce zuciyar Shugaba Bola Tinubu tana tare ƴan Nijeriya da halin raɗaɗin da suke fuskanta sakamakon tsare-tsaren gwamnati.

Mataimakin Shugaban ƙasar ya bayyana cewa, taron dama ce ta mayar da Nijeriya a matsayin fage na samar da makamashi ta hanyar ruwa da iska wanda zai fitar da damarmakin zuba jari har na tsawon sama da Dala biliyan 410 daga yanzu 2060.

Ya ƙara da cewa, gwamnati tana ɗaukar matakan da suka dace wajen ganin ta cimma muradunta na farfaɗo da harkar tattalin arziƙi da bunƙasarsa acikin al’umma.

A ƙarshe, ya roƙi al’umma da su cigaba da bai wa gwamnatin tarayya goyon baya domin ganin ta cimma kyawawan manufofin da ta saka a gaba domin amfanin su da ma ƙasar baki ɗaya.

By Babaji