Matasa sun yaba wa tsohon minista, Injiniya Sambo Jaji kan ayyukan raya ƙasa a Taraba

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Matasa daga sassa daban-daban na Jihar Taraba sun bayyana jin daɗinsu tare da yaba wa tsohon Ministan Ayyuka da Gidaje, Injiniya Mu’azu Jaji Sambo, bisa irin namijin ƙoƙarin da ya yi wajen raya ƙasa da tallafa wa jama’a, musamman lokacin da yake riƙe da muƙamin minista a gwamnatin tsohon Shugaba Marigayi Muhammadu Buhari.
A cewar matasan, Injiniya Sambo ya nuna ƙwarewa da kishin ƙasa ta hanyar gina sabbin hanyoyi, gyaran tsofaffi, da samar da ayyukan yi ga matasa da ɗalibai. Baya ga haka, ya tallafa wa marayu, gajiyayyu, da kuma bayar da tallafin karatu ga waɗanda ke da burin ilimi amma suka rasa damar ci gaba.
Wasu daga cikin matasan da suka tofa albarkacin bakinsu a shafukan sada zumunta irin su Facebook da Tuwita, sun bayyana cewa Injiniya Sambo ya zama abin koyi ga shugabanni, kasancewar har bayan barinsa muƙami, bai daina ayyukan alkhairi ba.

Umar Jalo daga Jalingo ya ce, “Ai Engr. Mu’azu Jaji Sambo na daban ne a cikin shugabanni da aka samu a Taraba. Fatan Allah ya ba shi wani muƙamin da za a ƙara amfana sosai.”
Auwal Yusuf ma ya ce, “Eh gaskiya ya yi ƙoƙari sosai duk da ƙarancin lokaci da ya riƙe wannan matsayin amma ya yi amfani da shi ya yi hanyoyi wanda ga shi muna gani. Allah ya saka masa da alkhairi.”
Haka kuma Christopher Yirwana ya bayyana cewa, “A gaskiya ya yi ƙoƙari, Allah ya saka masa don manufansa mai kyau, Amin.”
Abdullahi Abubakar daga Zing ya ƙara da cewa, “Wallahi, Jaji ɗan arziki ne, mai kishin jiharsa da jama’a. Allah ya biya masa dukkan buƙatunsa.”
Wani matashi mai suna Abu Albany ya ce, “Ba ranan da bana bin hanyarsa da yayi daga DSS Office Jalingo zuwa kan Masallacin Juma’a Ambaliya. Ina masa fatan alheri da kuma sake samun muƙamin babban ministan ayyuka da gidaje.”
Matasa da dama sun bayyana cewa irin shugabanci nagari da jajircewar Injiniya Sambo wajen kawo cigaba a Taraba ya zama abin koyi ga sauran ’yan siyasa. Sun ce irin waɗannan shugabanni ne ake buƙata, waɗanda ke kawo ayyuka da ci gaba ba tare da son kai ba.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Naseeru Taneemu Annuree, ɗaya daga cikin ɗaruruwan matasa da suka amfana da shirye-shiryen tallafin tsohon ministan, ya bayyana cewa, “Tarihin Taraba ba zai taba rubutuwa dadai ba sai an haɗa da labarin tsohon Minista Sambo. Saboda ya samu dama, ya amfanar da al’umma, shi ya sa al’umma ba za su taɓa mantawa da shi ba.”
Haka kuma shugaban ƙungiyar matasa ta MJS Like-Minds Youth Support Movement, Usman Liman Kasimu, ya ce, “A kullum addu’a muke ga tsohon Minista Injiniya Sambo. Allah ya saka masa da alkhairi bisa ayyukan cigaba da ya kawo a Jihar Taraba da ma kasa baki ɗaya. Irin shugabannin da muke buƙata, masu aiki ba magana.”
Matasa da dama sun bayyana cewa irin shugabanci nagari da jajircewar Injiniya Sambo wajen kawo cigaba a Taraba ya zama abin koyi ga sauran ’yan siyasa. Sun ce irin waɗannan shugabanni ne da ake buƙata, waɗanda ke kawo ayyuka da ci gaba ba tare da son kai ba.
A halin yanzu, rahotanni daga kafofin sada zumunta sun nuna cewa tattaunawa da jinjina ga tsohon ministan na ci gaba, inda jama’a ke fatan Allah ya sake ba shi damar cigaba da hidima ga ƙasa da jiharsa ta Taraba.

By ukarofi