Zargin sauya sheka: APC a Zamfara ta musanta kafa kwamitin maraba da Gwamna Dauda

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar All Progressives Congress APC reshen Jihar Zamfara ta bayyana labaran dake yawo cewar ta kafa kwamitin karɓar Gwamnan Jihar Dr. Dauda Lawal a matsayin soki burutsu da Kuma ƙirƙira Karya tsagwaron ta.

Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar na jihar, Yusuf Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa Blueprint Manhaja yau Lahadi a Gusau babban birnin Jihar.

A cewar sanarwar, rahotannin sun nuna rashin kishin ƙasa da ƙage ta hanyar munanan manufofin marubuta da kafafen yaɗa labarai.

Ya ce, jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ba ta taɓa tunkarar jam’iyyar PDP ko gwamnanta a jihar kan duk wani yunƙuri na neman gwamnan ya koma APC ba.

“Jam’iyyar APC ba ta goyon bayan ƙarya ta hanyar amfani da yanar gizo”

Sanarwar ta kuma bayyana cewa jam’iyyar APC na da kafafen hanyoyin sadarwa da yaɗa labarai kuma ta yi watsi da rahoton gaba ɗaya.

Jam’iyyar ta ci gaba da cewa za ta ci gaba da jan hankalin jama’a ta hanyar wayar da Kai don cigaban ta a jihar.

By ukarofi