DA Ɗumi-Ɗumi: ‘Yan sanda sun watsa barkonon tsohuwa ga ƴan zanga-zangar sako Nnamdi Kanu a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar AAC kuma ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowere da wasu ƴan gangamin neman sako Nnamdi Kanu, wato mai fafutukar kafa ƙasar Biafara, sun tsira a yayin da jami’an tsaro suka yi harbe-harbe ana tsaka da zanga-zanga.

A cewar DAILY POST, jami’an, waɗanda suka haɗa da ƴan sanda da sojoji sun fara sa ido ne akan zanga-zangar, wadda aka fara a safiyar yau Litinin.

An ga wani faifan bidiyo da ke nuna yadda ɗan gwagwarmayar tare da wasu masu zanga-zanga ke ƙoƙarin neman tsira daga harbe-harben jami’an tsaron.

Da fari ƴan gangamin sun ƙudiri aniyar yin tattaki ne zuwa Fadar Shugaban Ƙasa domin nuna buƙatar sako Nnamdi Kanu.

Daga bisani rundunar ƴan sanda ta gargaɗi masu shiryawa da kada su kusanci Fadar, wadda ake kira da Villa ko Aso Rock domin wata zanga-zanga.

By Babaji