Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Leƙen Asirin Soji ta Nijeriya (DIA) tana gudanar da bincike kan wani tsohon gwamna bisa zargin sa da ɗaukar nauyin sojoji da nufin yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu juyin mulki.
Majiyoyin Blueprint Manhaja sun bayyana cewa akwai zargi mai ƙarfi cewa tsohon gwamnan, wanda ɗan asalin yankin Kudu ne kuma tsohon babban jami’in gwamnati a ɓangaren albarkatun mai da iskar gas ne, ya ɗauki nauyin yunƙurin juyin mulkin, wanda da aka shirya aiwatarwa a ranar 25 ga watan Oktoban nan da muke ciki.
A ƙarshen mako ne kafofin watsa labarai na Sahara Reporters da Premium Times suka ruwaito cewa wasu hafsoshin soji 16, —waɗanda Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta ce sun shiga hannu saboda aikata abubuwan da saɓa ƙa’idar aiki— an tsare su ne saboda zargin su da yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Daga cikin sojojin da aka kama akwai wani mai muƙamin Birgediya-Janar da wani Kanar da wasu na ƙasa da su da ke Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro (ONSA).
Majiyar Blueprint Manhaja ta tabbatar da cewa akwai ƙamshin gaskiya a rahoton zargin yunƙurin juyin mulkin.
Majiyar ta ce, “Gaskiya ne. Akwai hannun fararen hula, ciki har da wani tsohon gwamna, kuma ana bincike domin gano irin rawar da suka taka a ciki. A halin yanzu, sojoji 16 da ake zargi suna tsare.
“Tsohon gwamnan da ke ake zargin tsohon mai babban muƙami ne a ɓangaren albarkatun mai da iskar gas, amma ba a riga an kai ga tabbatar da sa hannunsa a ciki ba.”
Wata majiyar kuma ta shaida mana cewa binciken na ƙoƙarin gano irin alaƙar da kuma tattunawar da ke tsakanin tsohon gwamnan da sojojin da aka kama.
Ta ƙara da cewa akwai yiwuwar za a gayyaci tsohon gwamnan domin amsa tambayoyi idan har aka samu ƙwararan dalilai game da alaƙarsa da sojojin da ake zargi da neman kifar da gwamnati.
Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar Leƙen Asirin Soji ce take gudanar da binciken, tare da wakilai daga rundunonin sojin ƙasa da sojin sama da kuma Sojin Ruwa ta Nijeriya.
“Mambobin kwamitin binciken sun haɗa da manya-manyan hafsoshin soji, bisa jagorancin wani mai muƙamin Manjo-Janar. An tsananta sirranta jerin sunayen waɗanda ake binciken.”
Majiyoyinmu sun bayyana cewa Manjo-Janar ɗin da ke jagorantar binciken ɗan asalin Jihar Neja ne.
“Akwai wani Kanar ɗan asalin wani babban gida daga Jihar Nasarawa. Mahaifinsa basarake ne kuma ɗan uwan tsohon Gwamnan Jihar, Umar Al-Makura,” in ji majiyar.
Binciken da muka gudanar a garin Lafia, hedikwatar Jihar Nasarawa, ya gano cewa zuri’ar Al-Makura suna cikin damuwa.
Ɗaya daga cikinsu da ya shaida wa wakilinmu a ranar Lahadi da dare, ya ce, wanda ake zargin “Kawuna ne. Gaba ɗaya danginmu sun shiga damuwa. Ni kaina ina cikin tashin hankali. Haka ma matar hafsan sojin. Addu’armu dai ita ce, Allah ya sa kada a kama su da laifin abin da ake zargi.”
Binciken da muka gudanar ya gano cewa an ƙara kama wasu sojojin domin amsa tambayoyi kan alaƙarsu da zargin yunƙurin juyin mulkin.
“Baya ga tsohon gwamnan akwai wasu manyan ’yan siyasa daga yankin Kudu da kuma Arewa da bibiyar duk wani motsinsu,” inji majiyarmu.
A ranar Asabar Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta fitar da wata sanarwa ta hannun Daraktan Yaɗa Labaranta, Birgediya-Janar Tukur Gusau, da ke ƙaryata rahotanni da ke cewa zargin yunkurin kifar da gwamnati ne ya sa aka dakatar da bikin zagayowar ranar samun ’yancin cikar Nijeriya karo na 65 a ranar 1 ga watan nan na Oktoba.
Manjo-Janar Tukur Gusau ya buƙaci jama’a da su yi watsi da labarin, yana mai bayyana masu yaɗa shi a matsayin maƙaryata kuma marasa kishin ƙasa.
Sanarwar mai taken ‘DHQ ba ta ambaci juyin mulki ba, ta ce, “DHQ ta lura da wani labarin ƙarya da wasu kafofin watsa labarai na intanet suka wallafa da ke riya cewa an soke bukukuwan zagayowar ranar cikar Nijeriya shekara 65 da samun ’yanci ne saboda zargin yunƙurin juyin mulki.
“Labaran suna nuni ga wata sanarwar DHQ na baya-bayan nan game da tsare wasu hafsoshin soji 16 da ake bincikar su kan saɓa kai’idar.
“Rundunar Tsaron Nijeriya na sanar da al’umma cewa abin da kafofin watsa labaran suka wallafa ƙarya ce tsagwaronta, kuma an ƙirƙira ta ce domin sanya mutane cikin fargaba da rashin yarda da juna.
“An yanke shawarar dakatar da bikin ne domin ba wa Shugaban Ƙasa damar halartar wani muhimmin babban taro a ƙasar waje da kuma ba wa sojijojinmu damar ci gaba da ragargazar a ayyukan ’yan ta’adda da ’yan bindiga da ke addabar ƙasar .
“Hedikwatar Tsaro tana kuma tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa binciken da ake yi kan hafsoshin sojan guda 16, abu ne na yau da kullum a gidan soja, domin tabbatar da ɗa’a da kuma ƙwarewa a kowane mataki.
“An riga an kafa kwamitin bincike yadda ya kamata kuma nan gaba za a sanar da al’umma sakamakon binciken.
“Hedkwatar Tsaro na kira ga ’yan ƙasa masu kishin zaman lafiya da su taimaka wa jami’an da duk wata gudunmawa da ta dace. Gwamnatin Tarayya da ɓangaren majalisa da ɓangaren shari’a suna aiki kafaɗa-da-kafaɗa domin tabbatar da tsaro da ci-gaba da kuma walwalar al’ummar Nijeriya da kuma ɗorawar tsarin dimokuraɗiyya.
“Hedikwatar tana kuma kira ga jama’a da su yi watsi da labaran ƙarya da maƙiyan wannan ƙasa suke yaɗawa. Rundunar tsaro ta Nijeriya ta tsaya kai da fata wajen tabbatar da biyayyarta da kuma kare kundin tsarin mulkin Nijeriya a ƙarƙashin jagorancin babban hafsan hafsoshin tsaro, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, GCFR.”
Tun bayan ɓullar labarin zargin yunƙurin kifar da gwamnati ’yan Nijeriya ke ta kira ga rundunar sojin ƙasar ta bayyana sunayen waɗanda ake zargin da ake tsare.
’Yan Nijeriya a kafofin sada zumunta sun buƙaci hukumomin soji su bayyana haƙiƙanin laifin da ake zargin hafsoshinta 16 da ta ce tana tsare da su.
Adelabi Gbenga, ya wallafa a Facebook cewa: “Zuwa ga rundunar soji, muna buƙatar ku sanar da ’yan Nijeriya haƙiƙanin laifin hafsoshi 16 kafin kunga,a da su. Ruwa ba ya tsami banza.”
“Saɓawa ƙa’idar aiki? Ku gaya mana me suka yi takamaimai. Kar ku sa mu a cikin duhu. Kuma da kuɗaɗen harajinmu ake biyan ku albashi,” inji Edidiong Jackson a kafar X.
Zakaria Olambeloye ya wallafa a Facebook cewa, “Su sojojin nan ko… Shi ya sa ba na son shiga aikin. Tun da mutane sun aikata laifi, ku fito ku faɗi irin laifin kuma shi ne wahala? Ku gaya mana su waye su, kuma wane laifi suka aikata.”
