Maryam Sanda za ta iya cigaba da zaman kurkuku bayan Antoni Janar ya nemi wasu hukumomi su binciki jaddawalin ɗaurarrun da Tinubu ya yafewa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Duk da cewa tana ɗaya daga cikin ɗaurarrun mutane 175 da Shugaban Bola Tinubu ya yi wa afuwa, wannan matar da aka yanke wa hukuncin kisa kan halaka mijinta, wato Maryam Sanda, ka iya cigaba da zama a gidan yari.

Haka na zuwa ne a yayin da Antoni-Janar na ƙasa kuma Ministan Shari’a, Frins Lateef Fagbemi ya umarci hukumomi da su yi nazari akan jaddawalin waɗanda aka yafewa gabanin aiwatarwa.

A shekarar 2017 aka yanke wa Maryam Sanda hukunci bayan samun ta da laifin kisan mijinta, Bilyaminu Bello, inda a kwanan nan ta shiga sahun mutanen da aka yafewa.

Saidai duk da haka, bincike ya nuna cewa da dama daga cikin ƴan jaddawalin afuwar har da Maryam ka iya fuskantar jinkiri bayan da aka nemi manya jami’ai da hukumomi su yi bincike akan kundaddakinsu.

Rahotanni sun bayyana cewa za a yi nazarin ne ƙarƙashin haɗakar hukumomin EFCC, NDLEA, ICPC da kuma rundunar ƴan sanda.

Majiyoyi sun shaida wa manema labarai cewa sama da rabin ƴan jaddawalin za a su fuskanci jinkirin ne a sakamakon nazarin.

Wani jami’i ya bayyana cewa akwai waɗanda aka yi kutsen sunayensu cikin jaddawalin ba tare da amincewar Fadar Shugaban Ƙasa ba, lamarin da yasa Antonin ya nemi a sake duba al’amarin kafin aiwatarwa.

By Babaji