Tinubu ya nemi majalisa ta tabbatar da Bernard Mohammed Doro a matsayin minista

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya aika wa Majalisar Dattawa sunan Dakta Bernard Mohammed Doro na jihar Filato domin ta tantancewa da tabbatar da shi a matsayin sabon minista a Majalisar Zartarwa ta ƙasa.

Matakin ya zo ne watanni kaɗan da aka zaɓi tsohon Ministan Jinƙai da Rage Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda Goshwe shi ma daga jihar a matsayin sabon Shugaban Jam’iyyar APC.

Dakta Doro, wanda aka haifa a yankin Kwall na Ƙaramar Hukumar Bassa ta jihar Filato a ranar 23 ga Janairun 1969, yana da gogewa ta fiye da shekaru 20 a fannoni da suka haɗa da aikin lafiya, kula da magunguna, shugabanci, da kuma ci-gaban al’umma a Nijeriya da ƙasar Biritaniya.

Ya yi karatu a fannoni da dama ciki har da ilimin magani (Pharmacy) da Shari’a (Law), tare da samun digirin kasuwanci (MBA) da ya mayar da hankali kan dabarun gudanarwa ta hanyar fasahar zamani, da kuma digiri na biyu a fannin aikin asibiti (Advanced Clinical Practice).

Kazalika, Doro ƙwararren ma’aikacin lafiya ne da ke da lasisi na bada magani kai saye (Independent Prescriber) da kuma na aikin asibiti (Advanced Clinical Practitioner) a tsarin kiwon lafiyar gwamnati na Biritaniya (NHS).

Haka kuma, ya yi aiki a asibitoci, cibiyoyin kula na gaggawa, da cibiyoyin lafiya na unguwanni (GP practices).

Baya ga aikin lafiya, yana da ƙoƙari wajen horar da matasa da kuma inganta al’umma a gida Nijeriya da ma ƙasashen waje.

By Babaji