JIBWIBS a Katsina ta shirya taron horar da malamai domin tabbatar da zaman lafiya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Iƙamatis Sunnah (JIBWIS) ta Jihar Katsina ta gudanar da taron horas da malamai da limamai daga yankunan da ke fama da matsalar tsaro, musamman inda aka samu yarjejeniyar sulhu da ‘yan bindiga.

An gudanar da taron ne a masallacin Juma’a na cibiyar horas da limamai da masu Khuduba ta Al-Wasil da ke kan hanyar Batsari.

Da yake jawabi yayin buɗe taron, sshugaban JIBWIS na Jihar Katsina, Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan (Sautus-Sunnah), ya ce manufar horaswar ita ce faɗakar da malamai da limamai kan muhimmancin tabbatar da zaman lafiya, haƙuri da juriya a cikin al’umma.

“Wannan shiri na nufin ilmantar da jama’a a rugage domin cusa ɗabi’un musulunci, ƙarfafa mutuntaka da wanzar da zaman lafiya bisa koyarwar Al-Qur’ani da Sunnah.” In ji Sheikh Yakubu Musa

Ya ƙara da cewa limamai da malamai suna da babban nauyi na jagorantar al’umma bisa gaskiya da bin koyarwar addinin Musulunci wajen magance rikice-rikice da tsananta wayar da kai.

Ya kuma jaddada buƙatar amfani da minbarin Juma’a da sauran kafafen yaɗa labarai wajen yaɗa sakon zaman lafiya, yafiya, da amana a tsakanin jama’a.

A nasa jawabin, mataimakin shugaban ƙungiyar na jiha, Alhaji Sani Abubakar Idris Daura, ya ce an shirya wannan zama ne domin fito da dabarun aiki da zai tabbatar da ɗorewar yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma da masu tayar da ƙayar baya.

Taron ya samu halartar wakilin kwamishinan ‘yan sanda da kwamandan NSCDC na jihar Katsina, tare da gabatar da ƙasidu da tattaunawa kan hanyoyin aiwatar da shirin a faɗin rugagen Fulani.

A cewar Yusuf Hassan Buhari, wanda ya fitar da sanarwar a madadin kwamitin yaɗa labarai na JIBWIS, ƙungiyar za ta ci gaba da shirya irin waɗannan taruka a sassa daban-daban na jihar domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya mai dorewa.

Ana ganin ɗaya daga cikin abinda ya ƙara yawaitar ta’addanci a jihar shine rashin ilimin addini daga ɓangaren ‘yan bindiga.

By ukarofi