
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya NAHCON, ta ƙaryata rahoton wata jarida da ke ikirarin Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh ya sa an tsare editanta bisa wallafa labarin rashawa da aka danganta wa hukumar.
A wata takarda daga mai taimaka wa Shugaban na NAHCON akan al’amuran gudanarwa, Ahmad Mu’azu, hukumar ta ce ta samu labarin na ƙarya da ake yaɗawa da nufin ɓatanci a gare ta da jagorancinta, lamarin da acewarsa, ba za su lamunta ba.
An wallafa rahoton ne a ranar 21 ga watan Oktoba, 2025, wanda aka yi wa laƙabi da ‘How NAHCON Chairman Used DSS To Detain Editor For Exposing Corruption, Pro-Shettima Reports’.
Mu’azu ya bayyana cewa rahoton ya ginu ne akan ƙarya da aka yi domin ɓata wa Shugaban hukumar suna da raina martabar hukumar.
Akan haka ne ya ce hukumar ta barranta kanta daga baki ɗaya zarge-zargen da rahton ya ƙunsa.
Ya ƙara da cewa, Farfesa Saleh Usman bai taɓa umarta ko neman a kama wani ɗan jarida ba ta hannun hukumar DSS ko wata hukumar tsaro.
Ya kuma ƙalubalanci jaridar da ta fitar da hujja gamsashshiya da ke nuna an tsare editan kuma da hannu shugaban na NAHCON.
