Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano
An bayyana shekaru sittin da tara na Jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya ta duniya, Engr. Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, a matsayin shekaru masu albarka da al’umma suka amfana da su ta fannoni daban-daban na cigaban rayuwa.
Shugaban ƙaramar hukumar Wudil, Hon. Abba Muhammad Tukur Utai, ne ya bayyana haka a sakonsa na taya murna ga Jagoransu, yayin da yake zantawa da manema labarai a gidansa dake garin Utai, inda ya jaddada irin gudunmawar da Kwankwaso ya bayar wajen cigaban al’ummar ƙasa.
Ya ce, “Da farko muna yi wa Allah godiya da muka ga wannan rana ta zagayowar haihuwar Jagoranmu Engr. Rabiu Musa Kwankwaso. Muna yi masa fatan alkhairi, Allah ya ƙara masa shekaru masu albarka, kuma duk abin da zai zamo alkhairi gare shi Allah ya haɗa shi da shi, wannan kuma sharri ne Allah ya kare shi. Muna yi masa fatan alkhairi a raguwar shekarunsa.”
Shi ma shugaban hukumar kula da ababen hawa ta jihar Kano, Dr. Faisal Mahmud, ya taya Jagoran nasu murnar cikar shekarun haihuwa, inda ya bayyana shi a matsayin shugaba abin koyi wanda ya amfanar da al’umma ta fannoni da dama. Ya kuma yi fatan Allah ya ƙara masa shekaru cikin lafiya da ƙarfi tare da baiwa Jagoran nasu damar jagorantar Nijeriya a zaɓe mai zuwa domin ci gaba da ceto al’umma daga halin matsin rayuwa.
A nasa ɓangaren kuma, Hon. Umar Musa Gama (Magi), mai ba wa Gwamnan Kano shawara kan sha’anin ciyarwa a makarantu, ya bayyana cewa suna farin cikin ganin wannan rana mai albarka, tare da fatan Jagoran nasu zai zama shugaban ƙasa a kakar zaɓe mai zuwa, ganin irin cigaban da ya kawo lokacin da yake gwamnan Kano domin sauran jihohin kasar su ma su amfana.
An dai gudanar da bikin murnar cikar tsohon gwamnan Kano, Engr. Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, shekaru sittin da shida da haihuwa, a gidansa dake kan titin Mila, Bompai, a birnin Kano. Bikin ya sami halartar manyan baki daga ciki da wajen jihar, ciki har da Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf, mataimakinsa Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo, kwamishinoni, masu ba da shawara, ’yan majalisu, shugabannin kananan hukumomi, da sauran manyan jami’an gwamnati.
