Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Masu halarta a taron wayar da kan matasa na waɗanda suka shahara a kafafen sada zumunta na kwana 2 Laraba da Alhamis, mai suna Kano Social Influencers Summit Karo na 6, sun buƙaci gwamnati ta fara amfani da fasahar basirar wucin gadi (Artificial Intelligence – AI) domin magance cin hanci da rashawa a matakai daban-daban na mulki.
Sun kuma jaddada buƙatar yin amfani da fasahar cikin ladabi, gaskiya da aminci, domin tabbatar da karɓuwarta a tsakanin al’umma.
Taron wanda aka gudanar mai taken: Yadda za a tafiyar da fasahar ƙirƙirarriyar ƙwaƙwalwa AI ba tare da an bar wata al’umma a baya ba, wato “Towards a More Inclusive Governance of AI,”
Taron ya haɗa masana daga jami’o’i, ƙungiyoyin farar hula, hukumomi da sauran al’umma.
Shugaban Kwamitin Amintattu na CITAD, kuma tsohon shugaban NCC, Mai Martaba Eze Ogbonna Ironmantu wanda Chief Nmezi Oguadinma ya wakilta, ya bayyana cewa amfani da AI yana ƙaruwa a Nijeriya, yana mai cewa fasahar za ta iya taimaka wa gwamnati wajen tabbatar da gaskiya a kwangiloli, dokoki da tsarin ɗaukar ma’aikata.
Shi ma a jawabinsa, jami’in hukumar National Data Protection Board, Abdulmalik Jamo, ya ja hankalin jama’a kan buƙatar kare bayanai yayin amfani da AI, yana mai cewa ana buƙatar tsare-tsare da doka mai ƙarfi don daidaita tsakanin buƙatar bayanai da kare sirrin jama’a.
A nasa ɓangaren, Dr. Bala Muhammad daga Jami’ar Bayero Kano ya bayyana cewa fasahar AI tana iya samar da labaran ƙarya da hotunan “Deepfake”, amma ita ce kuma za a iya amfani da ita wajen gano irin waɗannan abubuwa. Ya bukaci a ƙara wayar da kai da ilimin kafafen yaɗa labarai domin kaucewa mummunar illar fasahar.
Da ya je nasa jawabin, kwamishinan yaɗa labarai bayanai na jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Wayya, ya yi kira da a yi amfani da AI cikin gaskiya domin bunƙasa cigaba da tabbatar da gaskiya a cikin mulki,
Ya kuma ce gwamnatin Kano a shirye ta ke da ta kawo canji mai inganci da tasiri a fanni fasahar sadarwa a jihar Kano.
