Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Na san mai yiwuwa taken rubutun nan zai bai wa wani dariya. ƙila ma wani ya tambayi ko su waye kuma sojojin waya? To, in dai ka san su waye ake nufi da Sojojin Baka, ba za ka kasa gane Sojojin Waya ba.
Kamar yadda aka san Sojojin Baka da shiga tashoshin rediyo suna sayen fili don kare muradun wasu ko cin mutuncin wasu abokan hamayyar ubangidansu na siyasa, don ƙara angiza wutar adawa ko son a sani. Haka su ma sojojin waya suke yin nasu yaƙin ta zaurukan sada zumunta, suna rubuce-rubuce na ɓatanci ko aibata wani ko wasu da suke da saɓanin fahimta da su, ko don adawar siyasa, ko ma a dalilin wani bambanci na aƙida, ƙabilanci ko ɓangaranci.
Irin waɗannan matasa, har ma da dattijai, da suke bayar da kansu, lokacinsu da damarsu a matsayin ’yan amshin shatan wasu mutane da ba sa son a ji muryarsu ko a gansu a sahun gaba, suna cacar baki da wasu da ba sa ga maciji da su a siyasa, ko don suna so su ɓata wa wani suna a daina kallon sa da mutunci, suna haifar da damuwa sosai a tsakanin al’umma. Domin kuwa a maimakon yaɗa alheri, su jakadu ne na yaɗa saɓani, rabuwar kai, ko tayar da ƙura. Suna sayar da kimarsu da baiwarsu ta iya rubutu da tsara magana, wajen yi wa wasu aiki, don a riƙa ba su na cefane ko kuɗin data. Sam, ba sa damuwa da yadda suke ɓata sunan su a maimakon ɓata wani, ko nunawa duniya kansu a matsayin karnukan farauta, ba masu manufa ko ra’ayin kansu ba. Shi ya sa a taken rubutuna na kira su da masu fushi da fushin wani.
A wuraren da siyasa take da tasiri, kuma jama’a suke da wayewa kan al’amuran da suke faruwa a wannan fagen, kamar Jihar Kano, sojojin baka da na waya suna cin karensu babu babbaka. Har ma ana kallon su ne suke ƙara wa siyasa armashi, don suna bankaɗo wasu maganganu da batutuwa da ba kasafai ake tattauna su ba a fagen yaƙin neman zaɓe. Amma ko a nan ɗin ma suna wuce gona da iri, don akwai lokacin da sai da gwamnati ta kafa doka don taka wa masu wannan harka birki, saboda ƙalubalen da hakan ke haifar wa a zamantakewar al’umma da tsaro a jihar.
A jihohi irin su Filato kuwa, inda ake yawan samun kai ruwa rana tsakanin musulmi da kirista, sakamakon daɗewa da jihar ta yi cikin rikice-rikice masu nasaba da siyasa da ƙabilanci, irin waɗannan sojojin hayar, suna ba da gudunmawa ga hasala ƙalubalen tsaro da ake fuskanta, da ƙara hassala saɓani da rashin fahimta.
Ba abin mamaki ba ne ka ji muryoyin irin waɗannan matasa a kafafen watsa labarai na gwamnati da na masu zaman kansu, sun fito suna maganganu akan wasu ’yan siyasa, ko shugabannin al’umma, ko ma wasu manufofi na gwamnati, a inda suka saɓa da muradunsu ko ra’ayin ɗan siyasar da ya ɗauki nauyin su. Sau da dama suna yaɗa maganganu na rashin gaskiya ko masu karo da juna, ko masu haɗari ga tsaro, don kawai su karkatar da tunanin jama’a ko sanya kokwanto kan wani abu da ake so a yi, domin amfanin jama’a.
An yi amfani da irin waɗannan matasa a lokacin da ake cikin tsakiyar rikice-rikice a Jos, da lokacin da gwamnati ke shirin samar da wasu tsare-tsare da za su kawo zaman lafiya. Sai ka ji an biya waɗannan matasa sun shigo kafafen sadarwa suna ta maganganu na rashin tarbiyya da neman tayar da husuma a tsakanin jama’a, domin wannan shiri ya gurgunce kada ya yi nasara. Da yake kuma dama jihar cikin halin zafin aƙidar bambancin addini take, duk abin da aka danganta shi da addini ko ƙabilanci, yanzun nan za ka ga ya samu karɓuwa ana tattauna shi da ba da goyon baya. Wannan ya haɗa har da waɗanda ka ke yi wa kallon masu ilimi ne, ko masu kima ne a cikin al’umma. Amma da zarar irin wannan bambancin ya shigo sai ka ga an ware, kowa ya ɗauki matsayarsa, ko kuma kowa ya koma goyon bayan na gida. Koda kuwa abin da suke kai ba gaskiya ba ne!
A shekarun baya, ba na mantawa akwai wani lokaci da Mai Alfarma Sarkin Musulmi da kansa ya riƙa fitowa kafafen watsa labarai ko a wuraren tarukan jama’a yana tsawatar wa kan yadda sojojin haya na baka da na waya, ke haifar da firgici da rashin zaman lafiya a tsakanin ’yan Nijeriya. Yana mai cewa, hakan da suke yi yana nuna wa ’yan Nijeriya da ke zaune a ƙasashen waje cewa, ƙasa fa ba lafiya. Kamar ka ce, gobe za a tashi da yaƙi, tsakanin Musulmi da Kirista, ko tsakanin ’yan Arewa da ’yan Kudu.
Maganganu na ɓacin rai da rashin daɗi da ake yaɗawa a tsakanin ’yan ƙasa, saboda siyasa da ƙoƙarin cimma wani buri na addini ko ƙabilanci ba alheri ba ne ga ƙasar nan. Kuskure ne babba, shugabannin al’umma a dukkan matakai su riƙa kawar da kai ga abubuwan da ke faruwa a zaurukan sada zumunta, ko goyon bayan abin da ake yi, don hakan yana biya musu muradunsu. Alhalin abin da ba su sani ba shi ne, hakan na haifar da wasu irin matasa masu tsaurin ra’ayi, marasa kunya, da rashin girmama na gaba. Kuma irin su ne ke haifar da rashin jituwa da rashin sakewa da juna a tsakanin ’yan ƙasa, kowa na fargabar abin da ɗan uwansa zai aikata, saboda an sanya masa zargi da kokwanto a zuciyar sa.
Hakan harwayau, barazana ce ga cigaban tattalin arziƙi da kasuwanci, wanda ke razana masu son zuwa ƙasa ko cikin wata jiha su zuba jari. Domin yana nuna cewa dukiyarsu na iya fuskantar haɗari, a duk lokacin da fitina ta tashi, ko aka samu wata tarzoma. Sannan kamar yadda na faɗa a baya, ware wasu matasa ana ba su kuɗin data ko wani alawus, don su ci mutuncin mutane a waya, hatsari ne sosai. Don kuwa yana ƙyanƙyashe wasu gungu matasa ne masu tsattsauran ra’ayi, waɗanda idan abubuwa suka rincaɓe suna iya ɗaukar makamai su afkawa juna. Suna ƙara haifar da rabuwar kai da ƙara lalata alaƙa da cuɗanya a tsakanin ’yan ƙasa. Rikice-rikice na mu’amala da saɓani waɗanda ba sai an zubar da jini ba, ko an yi ƙone-ƙone ba, suna haifar da rashin natsuwa da rashin lafiya ƙwarin gwiwa, wanda a dalilin haka sai a yi ta samun koma baya.
Ci gaban al’umma ba ya samuwa a inda shugabanni ba sa gaya wa talakawa gaskiya, su ma kuma talakawa ba sa jituwa a tsakanin su, a inda ba a samun fahimtar juna da haɗin kai, a inda ake nuna wariya da bambanci, ko ake kallon wata al’umma a matsayin ƙasƙantacciya marar asali.
Lallai ne gwamnati ta tashi tsaye wajen gano irin mutanen da suke ɗaukar nauyin matasa masu haddasa rashin jituwa a tsakanin jama’a ta hanyar buɗe zaurukan sada zumunta, masu goyon bayan ƙiyayya da nuna wariya. Sannan a yi amfani da dokokin da aka kafa na kula da masu amfani da zaurukan sada zumunta, suna yaɗa gurguntattun ra’ayoyi na ta’addanci da rashin kishin ƙasa, domin hukunta masu yaɗa maganganu marasa dacewa da cancanta, saboda bambancin addini, siyasa, ko ƙabilanci.
Gwamnati ta yi amfani da ƙarfinta wajen matsantawa kamfanonin da suke gudanar da irin waɗannan manhajoji da ake buɗe zaurukan sada zumunta, irin su Facebook, ɗ, WhatsApp da sauransu, su rufe duk wani shafi da aka gano ana amfani da shi wajen cin mutuncin wasu, ko goyon bayan ta’addanci.
Lallai ƙungiyoyi irin su Arewa Media Writers da makamantansu su ƙara ƙaimi wajen aikin faɗakarwa da wayar da kan jama’a a kan illolin yaɗa maganganu masu haifar da rabuwar kai, yaƙi da yaɗa labaran ƙarya, da cin mutuncin mutane a zaurukan sada zumunta.
A ƙarshe, ina mai jan hankalin matasa ’yan uwana, su daina yarda wasu baragurbin ’yan siyasa suna amfani da su, don cimma son zuciyar su, su kuma ana suna ɓata makomarsu da kimar su a wajen jama’a, da rayuwar su ta gobe.
