Daga RABIU SANUSI
Kungiyar mata ta ‘Society of Women in Taxation’ (SWIT), wacce ke ƙarƙashin Chartered Institute of Taɗation of Nigeria (CITN), ta shirya taron kwana ɗaya a Kano domin tattauna batutuwan sauye-sauyen haraji, daidaiton jinsi, da kuma wayar da kan jama’a kan lafiyar kwakwalwa.
Taron wanda aka gudanar a dakin taro na Grand Central Hotel dake Kano ya haɗa masana, klƙwararru da membobin fannin haraji don tattauna tasirin sauye-sauyen haraji na kasa da yadda suke shafar daidaiton jinsi da ci gaban ƙasa gaba ɗaya.
A jawabin maraba da ta gabatar, Shugabar ta SWIT ta making Kasa Dr. Caroline Ndubuisi ta jaddada muhimmancin bai wa mata dama a harkar gudanar da haraji da kuma samar da manufofin haraji masu Kyau da ke inganta daidaito tsakanin maza da mata.
Shi ma a jawabin shi Shugaban ƙungiyar kuma Shugaban Majalisar CITN, Mr. Innocent C.Ohagwa, FCTI, a jawabin buɗe taron,ya yaba wa SWIT bisa rawar da take takawa wajen tattaunawar ƙasa kan harkokin haraji da sauye-sauyen da ake gudanarwa, yana mai cewa tsarin haraji mai haɗa kowa yana taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.
A cikin takardar da ya gabatar mai taken “Dokar Sauye-sauyen Haraji da Tasirinta ga Daidaiton Jinsi,” Shugaban Hukumar Haraji na Jihar Kano (Kano State Internal Revenue Service), Dr.Zaid Abubakar, ya yi bayani kan yadda sauye-sauyen haraji na baya-bayan nan za su iya taimakawa wajen ƙara samun haɗin mata a harkokin tattalin arziki da yanke shawarar manufofi.
Sauran gabatarwar sun haɗa da “Haɗin Kai Tsakanin Sauye-sauyen Haraji da Haɗaɗɗen Kuɗi (Financial Inclusion)” wanda Dr. Bashar Musa Idris, FCA, ya gabatar, da kuma “Cututtukan Hankali” daga Dr.Nusaiba Abdullahi Sa’id, wacce ta yi nuni da muhimmancin kula da lafiyar kwakwalwa musamman ga kwararru masu aiki a fannonin da ke da matsin lamba kamar na haraji.
An kammala taron da jawabin godiya da rufe taro daga Kwararriyar Ko’odinetar SWIT ta Jihar Kano, Hajiya Maryam Yahya Fagge, FCTI, wacce ta gode wa mahalarta bisa halartar su tare da sake jaddada ƙudirin ƙungiyar na inganta sana’a, ci gaban al’umma, da faɗakarwa.
Taron ya kare da ɗaukar hotunan taro, cin abinci tare, gabatar da takardu, bayar da lambobin yabo da kuma tambayoyi da amsoshi.
