Sowore da lauyan Nnamdi Kanu sun shaƙi iskar ƴanci daga kurkukun Kuje

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma ɗan gwagwarmayar fafutukar kare haƙƙin ɗan-adam, Omoyele Sowore tare da lauyan Nnamdi Kanu, sun samu ƴanci a yammacin jiya Litinin bayan shafe kwanaki huɗu a gidan yarin Kuje da ke Birnin Tarayya Abuja.

Sowore ya bayyana haka ne ta shafinsa na X inda ya ce, ya samu fitowa daga kurkukun bayan tsare shi ba bisa doka ba na tsawon kwanaki huɗu.

A makon da ya gabata aka tsare shi bayan ya halarci zaman shari’a a Kotub Majestare da ke Kuje.

An ga yadda Sowore da masu goyon bayansa ke rera waƙar murnar fitowarsa jim-kaɗan da sako shi a wani faifan bidiyo.

Tun a ranar Juma’a kotun ta bada belin Sowore tare da wasu mutane 11 ciki har da lauyan Nnamdi Kanu, wato Aloy Ejimkor da ɗan uwan Kanu, Emmanuel Kanu bisa zanga-zangar neman sako jagoran fafatukar kafa ƙasar Biafaran.

Kasancewar ba a cika sharuɗɗan belin ba, ƴan sanda suka sake tasa ƙeyar Sowore zuwa kurkukun domin kammala aikinsu, kamar yadda kakakinsu, Benjamin Hundeyin ya bayyana a wata sanarwa.

By Babaji