Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Sabbin alƙalai da aka rantsar su ne Abubakar Mohammed Dikko da Maryam Umar Abdullahi ɗaya ga tsohon babban alƙalin kotun ɗaukaka ƙara na ƙasa mai shari’a Umar Abdullahi,sai shamsuddeen Abdulrahaman Yanmama.
A jawabinsa ga sabbin alƙalai, Gwamna Raɗɗa ya jaddada girman amanar da aka ɗora a wuyansu, yana mai nanata muhimmancin kiyaye manyan ƙa’idodin shari’a na gaskiya, adalci, da amana a aikinsu ga jama’ar Jihar Katsina.
Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa, gwamnatin sa za ta ci gaba da tallafa wa bangaren shari’a tare da kare cikakken ‘yancin sa.
Ya bayyana cewa, zaɓin sabbin alƙalai ya biyo bayan tantancewa da amincewa, domin tabbatar da cewa waɗanda suka dace da hali nagari da ƙwarewa a fannin shari’a ne aka ɗaga zuwa matsayin alƙalai na babbar kotu.
Taron rantsuwar ya samu halartar manyan baƙi, ciki har da babban alƙalin Jihar Katsina.
‘Yan majalisar zartarwa ta jiha, ‘yan majalisar dokoki, sarakunan gargajiya, iyalai da abokan sabbin alƙalai.
