Da SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Wani ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Maradun a majalisar dokokin Jihar Zamfara, Hon. Maharazu Salisu Faru, ya sauya sheka daga Jam’iyyar sa ta Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC) a Jihar Zamfara.
Da yake sanar da shawarar sa a hedikwatar APC da ke Gusau a yau Talata, Hon. Faru ya bayyana cewa rashin gaskiya, adalci, da daidaito a cikin gwamnatin da PDP ke jagoranta a jihar, su ne wasu daga cikin dalilan da suka sa ya fice daga jam’iyyar sa ta PDP.
Ya yi zargin cewa gwamnatin da PDP ke jagoranta a Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin gwamna Dauda Lawal ta mayar da mazaɓar sa saniyar ware ta fannin cika alƙawuran kamfen ɗinsa, a ƙaramar hukumar ta Maradun tun lokacin da aka kafa ta.
Ɗan majalisar ya yi ikirarin cewa halin da gwamnatin PDP ke nunawa mazaɓar sa shine babban dalilin da ya sa ya yanke shawarar komawa APC.
A cewarsa, ya shiga APC ne don kawo sauyi mai ma’ana da ci gaba ga mutanen Jihar Zamfara.
Hon. Faru ya bayyana cewa ya ƙuduri aniyar yin aiki tuƙuru don tabbatar da nasarar APC a zaɓen 2027 a jihar.
Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Hon. Tukur Ɗanfulani, yayin da yake karɓar waɗanda suka sauya shekar, ya yi alƙawarin rungumar shi da jama’ar shi a matsayin halastattun ‘yayan jam’iyyar.
“Jam’iyyar za ta ɗauki kowa a matsayin halastattun ‘yayan jam’iyyar a jihar”. Hon. Ɗanfulani ya bayyana.
Ya jaddada cewa jam’iyyar za ta dawo da ikon ta a shekarar 2027 a jihar.
“Za mu sake tsara jam’iyyar mu domin nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu kuma da yardar Allah, APC za ta amshi Jihar Zamfara a shekarar 2027 dake tafe”. Hon. Ɗanfulani ya ce.
Ya buƙaci ‘yayan jam’iyyar ta APC a jihar, da su cigaba da bin doka da oda tare da hada kai don tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaɓen 2027.
