Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya amince da naɗa tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya kuma Marusan Katsina, Sanata Hadi Sirika a matsayin sabon Shugaban Hukumar Gudanarwar Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina.
Sakataren gwamnatin jihar Katsina Barista Abdullahi Garba Faskari wanda ya sanya hannu a takardar ya bayyana Hadi Sirika a matsayin mutum mai ƙwarewa da jajircewar a duk muƙaman da ya rike a gwamnati wanda hakan gwamna Dikko Raɗɗa ya ga dacewar sa da muƙamin.
Barista Abdullahi Faskari yayi fatan tsohon Ministan zai yi amfani da ƙwarewar sa wajen ciyar da jami’ar Umar Musa Yar’adua gaba.
Hadi Sirika ɗan shekara 61 da haihuwa an haife shi a ƙauyen Dubawa a Sirika na ƙaramar hukumar Dutsi a jihar Katsina.
