Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta dakatar da babban taron PDP

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Abuja, ta hana babbar jam’iyyar adawa ta PDP gudanar da babban taronta na ƙasa da take shiryawa, wanda ta tsara yi a ranakun 15 da 16 na watan Nuwamba a birnin Ibadan na Jihar Oyo.

Mai Shari’a James Omotosho yayin gabatar da shari’ar ya ce mambobin jam’iyyar uku ne da ke ganin an yi musu rashin adalci suka shigar da ƙarar.

Ya ce, hujjar da aka gabatar masa ta nuna cewa PDP ta bijire wa wasu daga cikin dokokin ƙasa, gyaran 1999 da sharuɗɗan hukumar zaɓe (INEC).

Omotosho ya bayyana cewa, jam’iyyar ta gaza yin sahihan tarukan jihohi gabanin yin babban taro na zaɓen ofisoshinta na ƙasa.

Don haka, kotun ta umarci PDPn da ta koma ta bi dukkan ƙa’idodi da doka ta gindaya mata, sannan ta kuma fitar sanarwa kwana 21 kafin ranar da ta zaɓa domin gudanar da taron.

A ranar Litinin PDP ta dakatar da tantance ƴan takararta na babban taron 2025 sakamakon wasu matsaloli na cikin gida.

By Babaji