‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da mataimakin kakakin majalisa na Kebbi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƴan bindiga sun yi garkuwa mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kebbi, Sama’ila Bagudu, a mahaifarsa da ke Ƙaramar Hukumar Bagudu ta jihar.

Majiyoyi sun ce ƴan bindigan sun kai farmaki ne a garin ranar Juma’a, inda suka yi ta harbe-harbe ba ƙauƙautawa, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici da tserewa domin neman mafaka.

A cewarsu, an yi garkuwa da ɗan majalisar ne jim-kaɗan bayan ya idar da sallah a wani masallaci a lokacin da ya nufi koma wa gida.

Babban Sakataren yaɗa labaran gwamnatin jihar, Ahmed Idris ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai.

Saidai, ba a samu ji ta bakin rundunar ƴan sandan jihar ba a yayin kammala haɗa rahoto.

By Babaji