PDP ta bijire wa umarnin kotu, ta cigaba da shirye-shiryen babban taronta

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babbar Jam’iyyar adawa, PDP ta ci alwashin cigaba da shirye-shiryenta na gudanar da babban taronta na ƙasa da ta tsara yi a ranakun 15 da 16 na Nuwamba a Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo, duk da cewa kotu ta fitar da umarnin dakatar da shi.

Hakan na zuwa ne ƙasa da sa’o’i 24 da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta hana PDP da Hukumar Zaɓe (INEC) yin taron ko karɓar kowane irin sakamako daga taron da aka shirya.

Mai Shari’a James Omotosho, ya hukunta cewa jam’iyyar ta taka dokarta ta tun farkon fara shirin taron, lamarin da ya yi sanadin dakatar da taron har sai ta cika ƙa’idodin da ake buƙata.

A yayin hukunci akan lamarin, kotun ta haramta wa jam’iyyar yin taron, sannan ta umarci INEC da kada ta karɓa ko ta wallafa ko amincewa da sababbin jagororin da za a zaɓa a taron har sai jam’iyyar ta cika sharuɗɗanta na cikin gida.

A wata takarda da Sakataren yaɗa labaran PDP na ƙasa, Debo Olugunagba ya fitar a yammacin jiya Juma’a, ya yi watsi da hukuncin, inda ya bayyana shi a matsayin ‘cin zarafin harkokin dimukraɗiyyar Nijeriya’.

Ya ce, hukuncin bai haramta musu ƴanci ko ikon cigaba da shirye-shiryen taron ba.

Jam’iyyar ta kafa hujja da wani hukunci da Kotun Ƙoli ta yi da ke tabbatar da cikakken ikon jam’iyyun siyasa akan gudanar da al’amuransu na cikin gida, yana mai kira ga mambobi da su cigaba da kasancewa a shiri.

By Babaji