Ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Nijeriya, inji Donald Trump

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A jiya Juma’a Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce al’ummar addinin Kiristanci suna fuskantar barazana a Nijeriya, lamarin da acewarsa ya sa zai sanya ta a sahun ƙasashen da ake da damuwa akansu.

Ya ce, kawo yanzu an halaka dubunnan Kiristoci a ƙasar, wanda yana faruwa ne sakamakon ta’addancin masu tsatstsauran ra’ayin addinin Islama, kamar yadda ya wallafa a wani rubutu a shafinsa na dandalin Truth Social.

A cewar jaridar Reuters Daily, Shugaban na Amurka ya sanya Nijeriya, wadda ita ce ke kan gaba wajen samar da albarkatun mai a sahun ƙasashen da ake tauye ƴancin yin addini cikin salama, wanda ke haifar da kisan gilla ga al’ummomi daban-daban musamman na Kiristanci.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida na Amurka ta zayyano waɗansu ƙasashe da ire-iren kashe-kashen ke faruwa waɗanda suka haɗa da Chana, Myanmar, Koriya ta Arewa, Rasha da Pakistan da sauransu.

Tuni Trump ya umarci wakilan Amurka Riley Moore da Tom Cole da kwamitin kasafin kuɗaɗen gwamnati na majalisar wakilai da su sanya ido da yin bincike akan al’amarin tare da aiko masa da rahoto.

A kwanakin baya ne wani sanatan Amurka ya yi zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Nijeriya, batun da gwamnatin tarayya ta musanta.

By Babaji