
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Al’amura na ƙara ƙazancewa a yau Litinin a Hedikwatar Babbar Jam’iyyar adawa (PDP) da ke Abuja, yayin da ƴan ɓangaren Ministan Abuja, Nyesom Wike suka yi yunƙurin karɓe iko da sakatariyar jam’iyyar.
Rahotanni sun bayyana cewa hakan wani ɓangare ne da nuna ƙamarin rikicin PDP, wanda ke fuskantar rarrabuwar kan ƴaƴanta tun bayan shan kaye a zaɓen 2023.
A kwanan nan ne ƴan ɓangaren Wiken suka sanar da naɗin Muhammad Abdulrahman a matsayin muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa biyo bayan dakatar da wasu manyan jami’an PDPn daga ɓangarorin biyu.
Da fari, Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC) ƙarƙashin jagorancin Umar Damagum ya dakatar da tsohon Sakataren jam’iyyar, Sanata Samuel Anyanwu da wasu jami’ai da ake ganin ƴan ɓangaren Wike ne.
Akan haka ne ƴan tsagin Wike suka sanar da dakatar da Damagum da wasu jiga-jigan jam’iyyar kan zargin su da rashin iya gudanar da jam’iyyar bisa inganci da durƙusar da muryarta a siyasance.
Da yake ganawa da ƴan jarida gabanin shiga hedikwatar a ofishin jam’iyyar, Abdulrahman ya ci alwashin dawo da ladabtarwa da haɗin kai acikin jam’iyyar, wanda shugabancin jam’iyyar ya gaza samarwa.
