Barazanar harin Amurka: Ribaɗu ya gana da jagororin tsaro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yammacin yau Litinin Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (NSA), Nuhu Ribaɗu, ya jagoranci zaman gaggawa da ya ƙunshi jagororin tsaro da na hukumomin leƙen asiri a Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta ƙasa (NCTC) a Abuja.

An gudanar da zaman ne da nufin nazari akan tasirin kalaman Shugaba Donald Trump na Amurka na kwanan nan akan Nijeriya.

A cewar rahotanni, zaman ya kuma ƙunshi jin ba’asin jagororin tsaron da na cibiyoyin leƙen asiri domin yin karatu na musamman akan ƙalubalen da kalaman Shugaban Amurkan ka iya haifarwa.

Da yake jawabi jim-kaɗan bayan zaman, Darakta Janar na Hukumar Wayar da kan Al’umma na ƙasa, Lanre Issa-Onilu ya ce ofishin NSA da manyan hafsoshin tsaro za su gana da manema labarai a yau Litinin.

Ya bayyana ikirarin Trump a matsayin ƙarya mara tushe da kuma gazawar sashen leƙen asiri na ƙasar.

Issa-Onilu ya ƙara da cewa, Gwamnatin Tarayya tana aiki tuƙuru wajen yaƙar ta’addanci, yana mai kira ga gidajen jaridu da su riƙa ruwaito labarai akan lamuran tsaro bisa inganci.

Tun ranar Juma’ar da ta gabata ne Trump ya ayyana Nijeriya a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da ake da damuwa akansu bisa zargin yi wa Kiristoci kisan gilla a sassan ƙasar.

By Babaji