Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
An sami ƙarin Naira biliyan 66 a ɓangaren Ilimi a kasafin kuɗin 2026 idan an kwatanta da Naira biliyan 90 da aka ware wa ilimi a shekarar 2025.
Ma’aikatan ayyuka,gidaje da sufuri ta sami Naira Biliyan 117 sai aikin gona da ya sami Naira biliyan 78.
Kiwon lafiya kuwa ya sami biliyan 67.5,haka kuma fannin ruwan sha ya sami Naira biliyan 62.8.
Sai ma’aikatar muhalli da ta sami Naira biliyan 53.8 sauran ma’aikatu da hukumomi suka sami Naira biliyan 536.384 dai dai da kashi 59.7 bisa ɗari na kasafin kuɗin.
Kwamishinan tsare-tsare da kasafin kuɗin Malam Malik Anas ya bayyana wa manema labarai haka a lokacin da yake bayani dalla dalla yadda aka kasafta kasafin kuɗin na 2026.
Ya ce kasafin kuɗin da aka sanya wa suna “Gina Al’umma Kashi na uku ya mai da hankali wajen cigaban al’umma.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya gabatar da kasafin kuɗi na Naira biliyan 865.8 inda Kashi 81 bisa 100 zai tafi a manyan ayyuka.
