Gwamnan Katsina ya kafa kwamitin da zai sa ido kan almajirai

Spread the love

Sakataren gwamnatin jihar Barista Abdullahi Garba Faskari wanda ya ƙaddamar da kwamitin a madadin gwamnatin jihar ya ce zai gudanar da bincike da kuma kawo mafita kan matsalar mutane da ke yawon bacci a kan tituna da wuraren da ba su dace ba.

Ya ce gwamnati ta ɗauki matakin ne domin ganin an rage yawan mutanen da ke kwana a waje saboda talauci, rashin gida, da kuma wasu matsalolin rayuwa.

Barista Faskari ya bayyana cewar Kwamitin zai fara gudanar da bincike da tattara bayanai domin gano mutanen da ke yawo ko kwana a tituna a dukkan ƙananan hukumomi na jihar tare da sama masu wuraren kwana na wucin gadi a yayin da za a cigaba da gudanar da sauran shirye-shiryen da taimakon da suka dace.

“kwamitin zai cigaba da kula da lafiyar jiki da ta ƙwaƙwalwar waɗannan mutane tare da tallafa musu wajen dawowa cikin al’umma,”inji Faskari.

Har wayau ya ce Kwamitin zai tsara shirin horar da waɗanda aka tarar da su a hanyoyin ƙananan sana’o’i domin su samu hanyar dogaro da kai tare da cigaba da wayar masu da kai

Haka kuma Kwamitin zai cigaba da haɗa kai da ƙungiyoyi da masu ruwa da tsaki domin su shigo ciki don ganin an daƙile matsalar a duka faɗin jihar a cewar sakataren gwamnatin jihar.

By ukarofi