Gwamnatin Kaduna ta bada damar samun ilimi da lafiya ga yankunan ƴan bindiga jihar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kaduna, Malam Ahmed Maiyaƙi ya bayyana cewa a yanzu gwamnatin jihar ta ba wa ƴan bindiga damar samun ilimi, lafiya da damarmakin harkokin rayuwa a matsayin ɓangare na kawo ƙarshen ayyukan kashe-kashe da garkuwa da mutane na tsawon shekaru a jihar.

Ya bayyana haka ne a lokacin taron kara wa juna sani kan aikin jarida na zaman lafiya da tawagar maruwaita na Ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa (NUJ) suka gabatar a Kaduna da haɗin-gwiwar Gidauniyar Zaman Lafiya ta ƙasa da Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta jihar.

A cewar Maiyaƙi, an samu cigaba daga fito na fito tsakanin su da jami’an tsaro zuwa tattaunawar sulhu da fifita hakan a matsayin mafita da ƙoƙarin ƙarshen amfani da ƙarfi ko tatsar kuɗaɗe.

Ya ce, an samar da salon ne da nufin dawo da zaman lafiya da inganta fahimtar juna a tsakanin al’ummar ƙauyuka domin kawo ƙarshen dukkan ayyukan ta’addanci a jihar.

Kwamishinan ya bayyana cewa, an yi nasara ne a lokacin da jagororin ƴan ta’adda suka nemi gwamnati ta sake buɗe kasuwanni, makarantu da cibiyoyin lafiya da aka rufe a baya saboda rashin tsaro.

Maiyaƙi ya ƙara da cewa tsakanin 2015 da 2023, jihar Kaduna ta samu rahotanni matsalolin tsaro guda 1,160 da suka yi sanadin mutuwar mutane 4,876da kuma garkuwa da dubunnai ko ɗaiɗaita su.

Kazalika, ya ce a 2021 kaɗai an rasa rayuka 1,192 da garkuwa da 3,348 abductions, lamarin ya tilasta rufe makarantu 142 da asibitoci 192.

By Babaji