Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
ƙungiyar Malaman jami’o’in Nijeriya, ta ASUU, ta mayar da kakkausan martani ga gwamnatin ƙasar, bayan ta zargi ministan ilimi, Dokta Tunji Maruf Alausa, da yin wasu bayanai masu cike da kura-kurai, dangane da batun cika alƙawuran da gwamnati ta yi a yarjejeniyoyin da ta ƙulla da ma’aikatan jami’o’in ƙasar.
ƙungiyar ta ASUU ta ce har yanzu romon baka kawai gwamnatin ƙasar ke yi wa ma’aikatan jami’o’i.
Ga dukkan alamu dai har yanzu tana kasa tana dabo, dangane da ja-in-jar da ke tsakanin gwamnatin Nijeriya da ƙungiyar malaman jami’o’in ƙasar, ta ASUU.
Rahotanni sun ambato ministan ilimi na Nijeriya, Dakta Tunji Maruf Alausa, na cewa, gwamnatin tarayya ta cimma nasarori cikin alkawuran da ta ɗaukar wa ma’aikatan jami’oin, kamar fara biyan kuɗaɗen shirin nan na tallafa wa ma’aikatan manyan makarantun ƙasar, da biyan bashin wasu alawus-alawus na malaman jami’o’i, da dai sauransu.
To sai dai ƙungiyar malaman jami’o’in ta ce ba ta gani a ƙasa ba.
Farfesa Ibrahim Tajo Suraj, shi ne shugaban reshen ƙungiyar na Jami’ar Bayero ta Kano, ya shaida wa BBC cewa sun ji maganganun da ministan ya yi to amma duk alƙawuran da ya ce an cika wa malama jami’oi su dai ba su gani ba.
Ya ce,” Sannan maganar sabunta yarjejeniya ma har yanzu ba a sabunta ba, haka batun biyanmu albashin na wata uku da rabi har yanzu shiru haka batun karin girma ma ba a yi ba, ariya-ariya ma ba a biya ba kai abubuwa da dama babu abin da muka gani, amma kuma sai gashi minista ya zo ya ce duka an biya, abubuwa kalilan ne gwamnati ta iya yi shima ba duka ba.”
ƙungiyar malaman jami’o’in ta ASUU dai tana ta kokantawa cewa, tun shekara ta 2009 take zama tana kulla yarjejeniyoyi da gwamnatin tarayya, amma har yanzu jifa ba ta dace da waiwaye ba, dangane da aiwatar da su yadda suka kamata.
ƙungiyar ta ASUU dai na son gwamnatin tarayya ta cika mata alƙawura da dama ciki har da batun sabunta yarjejeniyar da aka cimma tun 2009, wadda ta shafi yadda ake gudanar da ayyukan jami’o’i da yanayin aiki da kula da koyarwa.
Wannan yarjejeniya ta haɗa da batutuwan zamantakewar ɗalibai da ikon jami’o’i su gudanar da harkokinsu ba tare da tsoma bakin gwamnati ba wato da bai cin gashin kansu kenan.
Kazalika ASUU na son gwamnati ta Bayar da kuɗaɗen gudanarwa ga jami’o’i da Biyan su haƙƙinsu na aikin da suka yi a baya na wata uku da rabi da Biyan su cikon ƙarin albashin da aka yi wa malaman jami’a.
Sauran buƙatun da ASUU ke son gwamnati ta biya musu su ne Tabbatar da an tura kuɗaɗensu da ake cirewa daga albashinsu zuwa ƙungiyoyinsu da Biyan ƙarin albashi ga malaman da aka ƙara musu muƙami da kuma Dakatar da korar ma’aikatan jami’o’i ba bisa ƙa’ida ba.
