Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku, Dr. Adegboyega Oyetola, ya buƙaci gwamnatocin jihohin Yammacin Nijeriya su yi amfani da damar da tekun Leges–Kalaba ke bayarwa domin raya yawon shaƙatawa da sauran ayyukan kasuwanci na bakin teku, don haɓaka tattalin arzikin yankin.
Da yake jawabi a taron hulɗar gwamnati da jama’a na Yankin Kudu maso Yamma da aka gudanar a Akure, jihar Ondo, a ranar Laraba, 29 ga Oktoba 2025, Oyetola ya bayyana wannan babbar hanya ta bakin teku a matsayin aikin da zai sauya fasalin tattalin arziki da sadarwa a gaɓar tekun Nijeriya.
Ya ce, wannan shiri na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai buɗe sabbin damarmaki na kasuwanci, zuba jari da yawon buɗe ido, yana mai jaddada cewa lokaci ya yi da jihohin yankin za su ƙara zuba jari wuraren hutu, otel-otel, wuraren tarihi da al’adu domin amfana da wannan babbar damar tattalin arziki.
“Wannan hanya ta bakin teku ita ce jini na tattalin arziki da ke haɗa damarmaki, ƙirƙire-ƙirƙire da wadata,” inji shi. “Ina kira ga shugabannin jihohi da su mayar da hankali kan gina cibiyoyi, wuraren yawon shaƙatawa da dai-dai, domin al’ummominmu su amfana da ribar wannan gagarumin aiki.”
Oyetola ya yi bayanin cewa aikin zai kara haɓaka noman bakin teku, harkokin otel da yawon buɗe ido, bunƙasa kananan masana’antu, tare da ƙirƙiro sabbin al’ummomin kasuwanci daga Lagos zuwa Ogun, Ondo har zuwa gabar tekun gabas.
Ministan ya ce, yankin zai amfana matuƙa daga sabbin ayyukan yi, zuba jari da kuma wanzar da al’adu da albarkatun halitta da yankin ke da su.
Ya kuma yaba wa Shugaba Tinubu saboda faɗaɗa yankin ruwa na Nijeriya da kusan kilomita murabba’i 16,300, wanda ya ƙara tsayin ikon Nijeriya a teku da kimanin mil 20 na ruwa a wasu sassa.
Oyetola ya bayyana wannan nasara a matsayin mataki mai tarihi da zai ƙara wa Nijeriya ƙarfi wajen sarrafa albarkatun kasa a ƙarƙashin ruwan teku, buɗe sabbin hanyoyin bincike, zuba jari da makamashi daga teku.
Ya ce, faɗaɗa ikon ruwan ƙasar zai ƙarfafa zuba jari a harkokin jiragen ruwa, masana’antar ƙera jiragen ruwa, binciken teku da fasahar “blue economy,” abin da zai ƙara bunƙasa tattalin arzikin yankin na dogon lokaci.
A ƙarshe, Oyetola ya buƙaci haɗin kai mafi ƙarfi tsakanin Gwamnatin Tarayya da jihohi domin ƙara inganta tashoshin jiragen ruwa, tsaro a fagen ruwa, harkar kifi da ci gaban fitar da kaya ba tare da dogaro da mai ba.
