Gwamna Yusuf ya jinjina wa rundunar sojin Nijeriya bisa ƙoƙarin daƙile harin ‘yan bindiga a Kano

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa Rundunar Sojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro bisa hanzari da jajircewar da suka nuna wajen daƙile hare-haren ɓarayin daji da suka faru a wasu yankunan jihar a kwanakin baya.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Yaɗa Labarai na Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.

Gwamna Yusuf ya yi wannan magana ne lokacin da yake karɓar baƙon hanya, Babban Jami’in Kwamando (GOC) na Runduna ta 1 ta Sojin Nijeriya, Manjo Janar Abubakar Sadiƙ Muhammad Wase, a Fadar Gwamnati da ke Kano.

Manjo Janar Wase, wanda ya kai ziyara domin tantance yanayin tsaro a ƙananan hukumomin Shanono da Tsanyawa, ya bayyana cewa yana da alaƙa ta musamman da Kano, domin mahaifinsa, marigayi Colonel Muhammad Abdullahi Wase, ya taɓa shugabantar jihar a matsayin Sole Administrator a shekarar 1994.

“Ina nan ziyarar sanayya ce. Tun bayan karɓar ragamar Runduna ta 1, na kai ziyara wuraren da lamarin ya faru domin ganin yadda sojojimmu ke gudanar da aiki da kuma ƙarfafa musu gwiwa,” inji shi.

A nasa jawabin, Gwamna Yusuf ya gode wa Rundunar Soji bisa jajircewa da kishin ƙasa, tare da nuna godiya ga Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, saboda naɗa hafsoshi masu warewa da jajircewa wajen tabbatar da tsaro a ƙasa.

Don ara tallafa wa ayyukan tsaro a yankunan da abin ya shafa, gwamnan ya sanar da bayar da motocin Hiluɗ guda 10 da babura 60 ga Rundunar Hadin Gwiwa (Joint Task Force).

Gwamna Yusuf ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da mara baya ga hukumomin tsaro domin shawo kan matsalolin ’yan fashi, garkuwa da mutane, satar shanu da sauran laifuka da ke barazana ga zaman lafiyar al’umma a jihar.

By ukarofi