Kungiyar MODESA a Bauchi ta gano hanyoyin kama baburan hawa da aka sace a jihohin da ake rikici

Spread the love

Daga MU’AZU HARDAWA a Bauchi 

ƙungiyar dillalai masu sana’ar sayar da baburan hawa ta ƙasa reshen jihar Bauchi MODESA ta fito da sabbin hanyoyin magance satar baburan hawa a jihohin Nijeriya.

Shugaban ƙungiyar dillalan sayar da baburan hawa ta ƙasa reshen jihar Bauchi, Alhaji Muazu Chiroma shi ne ya bayyana cikin jawabinsa ga manema labarai bayan an sake rantsar da shi na tsawon shekara huɗu a karo na biyu.

Ya ƙara da cewa a halin yanzu sun fito da sabbin hanyoyin magance sayen baburan hawa na sata da ke fitowa daga wasu jihohin musamnan wuraren da ake fama da tashe-tashen hankula.

Yadda a halin yanzu suka daina sayen kayan da ke fitowa daga jihohi irin su Borno da Yobe saboda ana ƙwace abubuwan hawa na mutane a kawo jihohin da ake zaune lafiya don sayarwa.

Muazu Chiroma ya ƙara da cewa hukumomin tsaro na kiran su taron bita don ganar da su yadda ake sanin ɗanyen kaya don masu sana’a su tsira daga sharrin miyagun mutane.

Don haka ya ce a yanzu ƙungiyar ta fito da katin shaida wa ‘ya’yanta da kuma lambar abubuwan hawa ta masu sayarwa, wacce ake amfani da ita bayan an sayar da mashinan sai a cire a sayi lambar gwamnati.

Ya ce a halin yanzu sun fito da hanyoyin samun kuɗin shiga ta rasidin ƙungiyar da ake yankawa dukkan wanda suka sayi mashin don samun kuɗin shiga har samar wa gwamnati.

Alhaji Muazu Chiroma ya ƙara da roƙon Gwamna Bala Mohammed Abdulkadir ya taimaka musu don samun gina filin da aka basu a kasuwar Muda Lawal kamar yadda aka taimaki ‘yan kwantena masu sayar da wayar salula suka gina nasu.

Don a halin yanzu suna zaune a waje mai ƙunci da aikin hanya ya cinye a kasuwar central market.

Ya ce sun kashe sama da naira miliyan 20 amma har yanzu aikin bai je ko ina ba saboda girman wajen da kuma tsarin yadda suka ɗauko ginin.

An zaɓi sabbin shugabanni sama da talatin a matakin jihar Bauchi gabaɗaya.

Manya daga ciki sune Muazu Chiroma shugaba, Abdu Adamu Muazu Jama’are Ma’aji da Alhajiji Darazo Sakatare sai Alhaji Dan’asabe Idris PRO da kuma Alhaji Sanusi Bello Sakataren kuɗi.

By ukarofi