Rahoton da ke cewa an yi wa ɗan wasan Barau FC yankan rago ƙarya ne – ‘Yan Sanda

Spread the love

Wata sanarwa ɗauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce rundunar ta gargaɗi masu yaɗa ƙarya, tare da roƙon jama’a su yi watsi da rahoton baki ɗaya.

“Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Katsina ta samu labarin wani rahoto da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa an yanka wani ɗan kwallon kafa mai suna Nana Abraham, ɗan wasan Barau FC, ta hannun wasu magoya bayan Katsina United FC yayin wasan mako na 12 na NPFL da aka buga a filin wasa na Muhammadu Dikko a Katsina,” inji DSP Sadiq Aliyu.

Ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya ne, sharri ne, kuma ƙoƙari ne na tayar da hankalin jama’a da karya zaman lafiya da ake morewa a jihar, ya ce

DSP Sadiq ya tabbatar da cewa Nana Abraham yana cikin ƙoshin lafiya, kuma babu wata illa da ta same shi.

Binciken farko ya nuna cewa dukkan ‘yan wasa, ma’aikata, da jami’an da suka halarci wasan suna lafiya, kuma babu wani rahoton da ya nuna cewa an samu cikas ko tashin hankali tsakanin magoya baya da ‘yan wasa ko jami’ai kafin, yayin, ko bayan wasan biyo bayan matakan tsaro da yan sanda suka ɗauka.

Haka kuma, hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya (NPFL) ta gudanar da bincike kan abin da ya faru a wasan, ta gano wasu laifuffuka da ƙungiyar Katsina United FC ta aikata, ta kuma hukunta ta bisa ƙa’ida DSP Sadiq Aliyu ya ce.

A cewar sa cikin rahoton hukumar, babu inda aka ce wani ɗan wasa ya mutu.

Saboda haka, rundunar ta ke amfani da wannan dama ta gargaɗi masu yaɗa labaran ƙarya da sharri su daina, domin wannan laifi ne da doka ta haramta, kuma hukuncinsa yana da tsanani, jami’in hulɗa da jama’a ya bayyana haka.

Yayi gargaɗin cewa rundunar ba za ta yi wata-wata ba wajen kama da gurfanar da duk wanda aka kama yana yaɗa labaran ƙarya da ka iya tada hankalin jama’a.

Haka nan, ya roƙi jama’a da su dogara ne kawai da tushen sahihin labari, su kuma yi watsi da wannan rahoton da ba shi da tushe.

Ya bayyana cewa rundunar ‘yan Sanda ta Jihar Katsina, ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ‘yan Sanda, CP Bello Shehu, tana nan daram wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a duk faɗin jihar Katsina.

Wannan bayanin ‘yan sanda ya biyo bayan wasan gasar ƙwallon firimiya tsakanin ƙungiyar ƙwallon kafa na Katsina United da na Barau FC da aka tashi ci ɗaya da ɗaya a filin wasa na Muhammadu Dikko a Katsina.

To sai da hargitsi ya faru bayan tashi daga wasan inda ake zargin magoya bayan Katsina United tadawa.

By ukarofi