Kwamitin kasafin kuɗi na Majilisar Dokokin Katsina ya gudanar da taron jin ra’ayoyin jama’a

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Taron da kwamitin ya shirya akan kasafin kuɗin 2026 ya gudana ne a ɗakin taro na ƴan jarida na majalisar dokokin jihar.

Da yake buɗe taron, kakakin majalisar dokokin jihar Rt Hon Nasiru Yahaya Daura ya bayyana farin cikinsa bisa yadda ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki suka halarta tare da bayar da shawarwari masu ma’ana domin inganta kasafin kuɗin jihar.

A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na majalisar Hon Lawal H. Yaro (Away), ya bayyana cewa taron na daga cikin shirye-shiryen tabbatar da cewa jama’a suna da cikakken hannu wajen tsara da aiwatar da kasafin kuɗin jihar, domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen rabon albarkatun jihar.

Ya ƙara da cewa kwamitin zai yi duba da dukkan shawarwarin da aka gabatar kafin kammala rubuta kasafin kuɗin na 2026.

Shugaban kwamitin ya kuma jaddada cewa babu wata ma’aikata ko hukuma da aka sauya mata ranar gabatar da kasafin kuɗinta, don haka duk ma’aikata ko hukuma da ta gaza halartar zaman ba za ta samu wani abu a cikin kasafin kuɗin ba.

By ukarofi