Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar ƙididdiga ta Jihar Katsina (Katsina State Bureau of Statistics) tare da haɗin gwiwar UNICEF, ta ƙaddamar da horo na yini biyu a Katsina.
Horon na nufin koyar da shugabannin ƙananan hukumomin yadda za su riƙa amfani da bayanai (data) wajen tsara da aiwatar da shirye-shiryen rage talauci da inganta rayuwar jama’a a matakin ƙananan hukumomi.
A jawabinsa, kwamishinan ma’aikatar kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki, Malam Malik Anas , wanda Babban jami’in ƙididdiga na Jihar Katsina, Farfesa Saifullahi Sani Matazu ya wakilta, ya ce manufar taron ita ce ƙarfafa shugabanni wajen yanke shawara bisa hujjar bayanai domin kawar da talauci a tsakanin al’umma.
Shugaban hukumar ci gaban Katsina, Dr. Mustapha Shehu ya yaba da irin jajircewar hukumar ƙididdiga da UNICEF wajen shirya wannan taro, yana mai cewa yana da matuƙar tasiri ga ci gaban jihar.
Shi ma wakilin UNICEF ya bayyana jin daɗin sa bisa kyakkyawar alaƙa dake tsakanin UNICEF da Gwamnatin Jihar Katsina, tare da yabawa Gwamna Raɗɗa bisa jajircewarsa wajen yaƙi da talauci da tabbatar da walwalar yara.
Da yake buɗe taron, Gwamna Dikko Raɗɗa wanda kwamishinan raya karkara da ci gaban al’umma ya wakilta, ya jaddada cewa gwamnati za ta ci gaba da amfani da bayanai wajen tsara manufofin rage talauci da inganta rayuwar jama’a.
An gudanar da laccoci da tattaunawa kan batutuwan Child Poverty and Social Protection, da kuma Data-Driven Decision Making and Linking Evidence to Child Rights Programming.
Ƙananan hukumomi 34 ne suka halarci taron na kwanaki biyu a Katsina.
