Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Sam ba mu yi mamaki da wasu marar sa kishin ƙasa da ke zaman ‘yan kwangilar rusa Arewa su ka ɓarke da sowa kamar yadda a ke yi in an sha ƙwallo yayin da shugaban Amurka Donald Trump ya jefa sunan Nijeriya a bakin littafin Amurka da tuhumar yi wa mabiya addinin Kirista kisan kare dangi. Dama aikin ‘yan kwangila shi ne jawo fitina ta ‘yar gaba ɗaya ga Nijeriya musamman Arewa. Asalin wanda ya mika ƙorafi Amurka Bishop Wilfred Chikpa Anagbe ya na magana kan jihar Binuwe ne, ya yi ta bayanai har ya fake da wannan wajen nuna sauran jihohin ma haka ne kuma wai Musulmin Nijeriya na yunƙurin ƙaddamar da shari’a ko musuluntar da Nijeriya. Shin da gaske ne a na yi wa kiristoci kisan kare dangi a Nijeriya? Haƙiƙa duk kirista mai adalci zai ce sam ba haka ba ne zargin farafaganda ce kawai da za ta haifar da sharrin da zai shafi kowa.
Me ya sa wasu ke murna kan wannan barazana? A nan maganar ta ke. Nan biri ya yi kama da mutum. Mun sha bayyana cewa ‘yan kwangilar nan dama daga wannan yanki na Arewa ta tsakiya da su ka haɗa da kudancin Kaduna, Binuwai, Filato da can gefen Arewa maso gabar su ka fito. Tsiraru na Arewa maso yamma sun ayyana kan su da zama Hausawa na asali. Babu ko tantama mutanen nan ba Hausawa ba ne kuma cikin wannan aikin na su ne ma a ka kai ƙara Amurka da tunanin za ta yi dirar mikiya ga al’ummar Arewa ko daukar matakin da ka iya wargaza Arewa. Mu duba fitinar Sudan da Somaliya yanda a ka hargitsa ƙasashen tsawon shekaru. Ba ko raba-daya biyu haka ‘yan kwangila ke muradi ya faru da Arewa don rushe dukkan alamomin tarihi na gaskiya da gidajen sarauta da samun damar ɗauki dai-dai ga wasu mutane da ke hana iyayen ‘yan kwangilar rawar gaban hantsi.
Abun da na ke ƙara jan hankali a nan shi ne, dalilin tsananin kiyayyar ‘yan kwangila ga Hausawa shi ya sa su ka zaɓi shigar burtu su ka zama Hausawa don ta haka su ke muradin ingiza Hausawa su dau maƙami a shiga dauki ba daɗi a tsakanin musulmi da kuma cimma burin ƙirƙiro ‘yan ta’adda Hausawa. Lokacin da Lardin Arewa mai tsayin daka kan addinin Musulunci da Kirista ya zama sansanonin ‘yan gudun hijira, burin mutanen nan ya cika.
Mun gode wa Allah yanda gwamnatin Nijeriya ta yi watsi da wannan zargi na Amurka. Ma’aikatar wajen Nijeriya ta ce zargin na Trump ba daidai ba ne don Kiristoci na gudanar da addininsu a ko ina a cikin Nijeriya ba tare da katsalandan ba. Ba wanda a ke tsangwama a Nijeriya saboda addininsa. Ranar Jumma’a ka duba masallatai, ranar Lahadi ka duba majami’u wato coci-coci za ka tabbatar kowa na gudanar da ibadarsa ba tsangwama. Makiran da su ka kai kara Amurka makiya zaman lafiya ne kuma ‘yan Nijeriya masu kishin ƙasa ba za su yafe mu su ba.
Yanayin mulkin Trump ke bude irin wanman ƙofar don a wa’adin mulkinsa na farko a 2020 ma makamancin irin wannan tuhuma ta bijiro daga Amurka kan Nijeriya. Tambaya-shin akwai inda a duniya Kirista ke addininsu yanda su ke so da ya fi Nijeriya? Ni dai ban gani ba in kuma akwai wanda ya taɓa zuwa wata ƙasa musamman cikin nan Afurka ya ga ‘yancin addinin ta ya fi Nijeriya ya zo ya yi ma na bayani.
ME AMURKA ZA TA IYA YI YANZU
Idan wani na tsammani wannan na nufin Amurka za ta kawo hare-hare kan Nijeriya ne don haka ya ke murna, to ya fashe da kuka don ba haka lamarin zai kasance ba. Tun da zargin ƙarya ne to duk matakin da Amurka ta ɗauka na takurawa zai shafi kowa ne. Wane cigaba Iraki ta samu da Amurka ta kutsa can, wace riba a ka samu a Afghanistan da mutanensu su ka roki Amurka ta shigo? Kai ko nan Libya inda Amurka da Faransa su ka sa baki har gwamnatin Moammar Gaddafi ta faɗi, ai har yau ƙasar ba ta warke ba, wato an tashi daga targaɗe an koma karaya ko daga suma zuwa mutuwa duk da daɗi ne ya yi wa Libiyawa yawa su ka buƙaci a kashe Gaddafi ko za su kara more rayuwarsu.
Hannayen iyayen ‘yan kwangilar rusa Arewa ne ya bayyana ƙarara a kai ƙara Amurka don jawo fitina. Barayin daji tamkar iccen hura wuta ne na ‘yan kwangila, su kuma ‘yan kwangilar yanar gizo tamkar zuga-zugi ne na hura wutar fitina ta tashi balbal don kowa ma ya kone. Yo ba ku taɓa jin in wani ran sa ya ɓaci sai ya ce da kahon tashin alƙiyama na hannunsa da ya hura kowa ma ya san inda dare ya yi ma sa.
ALBIRINKU makiya Arewa wannan yaƙi da ku ke nema da ingiza fitina ta su Ouba Tibati ba zai yiwu ba. Hasalima nan ba da daɗewa ba duk wanda ya cigaba da zakewa dubunsa zai cika jami’an tsaro za su cafke shi don fuskantar tuhumar cin amanar kasa da ta’addanci. Gwamnati ai ba karya ba ce. Duk wanda ya raina matakan gwamnati na dawo da salama zai ɗanɗana kuɗar sharrin kwangilar da ya ɗauko. Illa iyaka.
Makiran farko ma yaya su ka kare balle na zamanin yau ‘yan wahala. Ko shi Trump zai sauka daga karaga kuma ai mun ga yadda tsohon shugaba Joe Biden ya yi watsi da wasu daga miyagun manufofin Trump. Duk tsawon dare gari zai waye.
Shin ta yaya bahaushe zai boye kan sa a Nijeriya in ba ƙaryar ‘yan basaja Hausawan ƙarya ba?
Don kare mutane da ba sa samun damar karance-karance musamman a labarun da a kan wallafa a yanar gizo, na jefa ƙalubale ga masu buɗe shafukan yanar gizo su na iƙirarin kare haƙƙin Hausawa inda su ke fakewa da hakan wajen aibanta Shehu Mujaddadi da manyan malaman Islama. Su kan yi amfani da alamu ko zayyanar karya a matsayin hotonsu. Waau ma na sanya hotunan tsoffin shugabannin kasa ko ma wasu dabbobi ciki har da ƙura. Kazalika sun ƙirƙiri sunaye masu kama da na Larabawa irin Haris, Sultan, Alhawsawi da sauransu. Su kan zayyana waɗannan shafukan da na gwagwarmaya. Bayan haka akasarin su kan rufe shafin bayanansu “locked profile” don tunanin kar a gane ko su waye ne. Alhali su na yin baya ba zani ne don ba a buya matukar za a hau yanar gizo.
Madugunsu na Kamaru mugun mutum mai kamfen ɗin kunna wutar fitina a Nijeriya Ouba Ali Mohaman ya rufe shafin bayanansa. Wannan shi ne alamar makirci da tabbatar da mutanen nan miyagun masu aikata laifi ne da ke tsoron kar a a cafke su don gurfanar da su gaban kotu.
Shin a Nijeriya akwai dalilin da zai sa Bahaushe ya buya don zai faɗi ra’ayinsa?
Sam babu wannan dalilin shi ya sa har zantawa a ke yi da malaman Hausa irin su Farfesa Aliyu Bunza kan tarihin Hausawa da martabar harshen. Mafi girman abun da masu iƙirarin Hausa zalla ke boyewa shi ne su ɗin wa imma ba Hausawa ba ne ko ba musulmi ba ne. Yau da za su bayyana kan su kamar yanda shi Bishop Wilfred ya yi da magana ta kare. Ai da sauƙi ka san waye abokin adawarka amma munafuki mai shigar burtu na da wuyar sha’ani don zai iya yin illa ga waɗanda ba su ankara ba sai an haska sosai kafin wani ya ankare.
Idan wanda ba Musulmi ko dan addnin gargajiya ya zagi Shehu Mujaddadi ba mamaki don akwai adawa ta zahiri da badini. Me haƙƙin mai bin addinin gargajiya ko wanda ba Musulmi ba kan jihadin Shehu da murde wuyan tarihi na hari kan sarki Makau wai a na sallar idi a Zaria? Ko taron sallar idin ma bikin al’adu ne? Ba zai yiwu wasu su riƙa shishshigi a lamuran addinin wasu a samu zaman lafiya ba. Mutunta juna shi ne maslaha.
KAMMALAWA
A batun ‘yan ta’addan daji na sha magana a kan su cewa ‘yan sharar fage ne na wannan kwangilar ta kunna wutar yaƙin ƙabilanci a tsakanin al’ummar Arewa da ke zaune lafiya. Daga dai yanda ‘yan kwangilar nan ke yayata miyagun labaru da fesa guba; ya nuna ba sa ƙaunar ta’addanci ya kare har sai sun kai ga kunna babbar wutar fitinar ƙabilanci. Irin wannan wuta ta na da wuyar kashewa gabanin asarar kisan kiyashi a tsakanin mutanen da ke zaune tare tsawon shekaru. ƙabilanci kan rufe idon mai yin sa ya koma son zuciya zalla. Don haka ko da ta’addanci ya kare za su cigaba da kunna wuta ta rashin mutuntawa ga mai alfarma Sarkin Musulmi da manyan sarakunanmu. Waɗannan fa ba su da asara don dama makiya al’ummar Arewa ne da ƙarfin imanin addinin su ya hana su ƙullawa abokan zama gadar zare da duk wani yanayi da zai haddasa zaman doya da manja. Hakanan zumuncin al’ummar yankin kan amfani hatta bako da ya zo don harkokin kasuwanci ko wasu lamura na zamantakewa.
Matuƙar mutanen nan sun cigaba da zama a ɓoye ta tabbata su na wata mummunar manufa da ya dace hukumomin tsaro su rore su don fuskantar shari’a. Haƙiƙa ba ruwan Hausawa da mutanen nan.
