An rasa rayuka bayan zanga-zanga ta ɓarke kan rashin tsaro a Malumfashi

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina 

’Yan bindiga sun addabi ƙauyen Danjanku da ke yankin ƙaramar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina da kai hare-hare, lamarin da ya sanya zanga-zangar neman mafita ta ɓarke a yankin, inda aƙalla mutane biyu suka rasa rayukansu.

Hare-haren na ’yan bindiga sun tilasta matasan yankin fitowa zanga-zanga ne, domin nuna fushinsu kan matsalar rashin tsaro. Zanga-zangar ta auku ne cikin ƙauyukan Danjanku, Dantashi da Dayi da suke ƙaramar hukumar Malumfashi a jihar ta Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa, zanga-zangar ta faru ne bayan sabon harin da ’yan bindiga suka kai a daren ranar Litinin, 10 ga Nuwamba, 2025.

Hare-haren ’yan bindigar ya yi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya da sace wasu 17, duk da yarjejeniyar sulhu da aka ƙulla da su.

Mazauna yankin sun bayyana cewa, harin na ranar Litinin shine karo na uku cikin mako guda, lamarin da ya kai adadin mutanen da aka sace zuwa sama da 30 a yankunan da abin ya shafa. Shaidu sun ce ‘yan bindigan sun farmaki ƙauyen Danjanku da misalin ƙarfe 12:00 na dare, inda suka tsallaka katanga suka shiga gidaje, suka yi garkuwa da mutane sannan kuma suka kashe mutum ɗaya.

Saboda fusata kan lamarin, matasa sun fito kan babbar hanya suna zanga zanga, inda suka toshe babban titin Funtua zuwa Katsina. Matasan sun nuna ɓacin ransu kan hare-haren da kuma gazawar gwamnati wajen samar da tsaro. Jaridar majiyar Blueprint Manhaja ta ce zanga-zangar da ta fara cikin lumana ta rikiɗe zuwa tashin hankali bayan da jami’an tsaro suka isa wajen domin tarwatsa su, inda ake zargin sun harbe mutane biyu har lahira tare da jikkata wasu mutum biyu.

Daga baya mazauna ƙauyukan Dantashi da Dayi suka shiga cikin zanga-zangar, inda suka toshe hanyoyi da kunna wa tayoyi wuta domin nuna ɓacin rai kan tabarbarewar tsaro.

By ukarofi